Gwamnan Zamfara ya ba JIBWIS N100m domin gina Jami’a a Jihar Jigawa?

Gwamnan Zamfara ya ba JIBWIS N100m domin gina Jami’a a Jihar Jigawa?

Jaridar Sahara Reporters ta fitar da rahoto cewa gwamnatin jihar Zamfara ta taimakawa kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a wa iqamatus Sunnah gudumuwa Naira miliyan 100.

Rahoton da jaridar ta fitar ya nuna cewa kungiyar musuluncin ta samu wannan kudi ne domin gina jami’ar addini a jihar Jigawa, a lokacin da jihar Zamfara ta ke cikin halin talauci.

Da Legit.ng Hausa ta yi bincike, ta gano cewa babu gaskiya a rahoton da ke yawo na cewa gwamnatin Zamfara ta bada kudi domin a gina jami’ar musulunci a jihar Jigawa.

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a Waikamatus Sunnah, JIBWIS ta na aikin ginin jami’ar Jigawa ne da kudin da ta tara daga cinikin fatun dabbobi da ta ke yi a lokutan bikin sallah.

A cewar wani babban jami’in kungiyar, a shekaru uku, JIBWIS ta tara fiye da Naira miliyan 260 wanda aka samu daga cinikin fatar raguna da shanu da za ayi amfani da su wajen wannan aiki.

Gaskiyar lamarin shi ne wata babbar makaranta ce ta gaba da sakandare za a gina a jihar Zamfara, ba jami’a ba. JIBWIS za ta gina wannan makaranta ne a karamar hukumar Shinkafi.

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya karyata rade-radin bada gudumuwa, ya kira rahoton da labarin bogi. Gwamnan ya bayyana wannan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

KU KARANTA: JIBWIS ta samu N100m daga hannun Gwamnan Jihar Zamfara

Gwamnan Zamfara ya ba JIBWIS N100m domin gina Jami’a a Jihar Jigawa?
Shugaban JIBWIS da Gwamnan Zamfara
Asali: Instagram

Ga abin da Matawalle ya fada: “Mun hada-kai ne da kungiyar JIBWIS wajen kafa babbar makarantar addinin musulunci a karamar hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.”

Ya ce: “Wannan cibiya za ta taimaka wajen fahimtar da addini ta hanyar koyar da musulunci a tsarin boko na zamani.”

Bayan haka, Bello Matawalle ya bayyana cewa tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa ya ba kungiyar gudumuwar gine-gine a Shinkafi wanda wannan cibiya za ta more su.

Alhaji Attahiru Bafarawa shararren mai kudi ne a Najeriya wanda ya ke da kishin addini da taimakon jama’a. Bafarawa ya yi mulki a jihar Sokoto tsakanin 1999 zuwa 2007.

Sai dai rahoton ya yi gaskiya da ya ce jihar ta na cikin inda aka fi fama da talauci a Najeriya. Alkalumun hukumar NBS sun tabattar da Jigawa da Zamfara a cikin fakiran jihohi.

Jihohin da ke sahun gaba a bangaren talauci a Najeriya su ne: Sokoto, Taraba, Jigawa, Ebonyi, Zamfara, Yobe, da kuma Adamawa. NBS ta ce talauci a Jigawa ya kai 87.02%.

Alal hakika, gaskiyar ita ce a jihar Jigawa kungiyar JIBWIS ta ke gina jami’a ba Zamfara ba, kuma gwamnatin Zamfara ba ta sa kudinta a wannan aiki da ake yi a makwabciyar jiha ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel