Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa kan ayyuka 774,000

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa kan ayyuka 774,000

- Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri na gaggawa kan hukuncin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya ba karamin ministan kwadago, Festus Keyamo goyon bayan aiwatar da shirin a ranar Talata

- Da farko dai majalisar dokokin tarayyar ta dakatar da shirin daukar ma'aikatan na musamman

A yanzu haka majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri na gaggawa kan hukuncin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000.

‘Yan majalisar dokokin tarayyar sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar ma’aikatan daga hukumar daukar ma’aikata ta kasa, wacce ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.

Sai dai, Keyamo ya fada wa manema labarai a ranar Talata, cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukace shi da ya ci gaba da shirin daukar ma’aikatan ba tare da la’akari da matsayar majalisar dokoki ba a kan lamarin.

Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa kan ayyuka 774,000
Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta shiga taron gaggawa kan ayyuka 774,000 Hoto: Spread
Asali: Facebook

Shugaban Majalisar dattawa, a farkon zaman majalisar na yau Laraba, ya yi kira ga ganawar sirri domin tattauna lamarin.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona

Ya yi hakan ne domin hana ‘yan jarida nadar tattaunawar wanda ka iya lalata dangantakar da ke tsakaninsu da bangaren zartarwa kan lamarin.

A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin daukar ma’aikata na musamman da majalisar dokoki ta dakatar.

Gwamnatin ta sanar da kaddamar da shirin ta shafinta na Twitter a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shirin wanda ma’aikatar kwadago ke jagorantar, daga cikin matakan rage radadin annobar korona.

Za a dauki mutum 1,000 daga kowani karamar hukuma 774 da ke kasar, sannan kwamitocin jiha za su kula da shirin.

“An kaddamar da kwamitocin zaben ma’aikatan na jiha kuma sun fara aiki,” cewar gwamnatin tarayya ta shafinta na Twitter.

Keyamo ya yi cacar baki da majalisar dattawa a kan cewar su za su tsara yadda daukar aikin za ta kasance.

Kwamitin majalisar tarayya a kan kwadago ya dakatar da fara diban aikin sakamakon hatsaniyar da ta shiga tsakaninsu da karamin ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel