Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona

Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona

- Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya (NLC), reshen jihar Taraba, Peter Gambo, ya rasu

- Gambo ya rasu ne a safiyar ranar Talata, 14 ga watan Yuli sakamakon cutar ta korona

- Har zuwa mutuwarsa, Peter Gambo ya kasance shugaban kungiyar NLC reshen jihar Taraba inda yake a zangonsa na biyu

Rahotanni sun kawo cewa shugaban kungiyar kwadago na Najeriya (NLC), reshen jihar Taraba, Peter Gambo, ya rasu.

Peter Gambo wanda aka killace a cibiyar killace masu cutar korona ta jihar Taraba da ke Jalingo, ya rasu ne a safiyar ranar Talata, 14 ga watan Yuli sakamakon cutar ta korona.

Hukumar asibitin ta tabbatar da lamarin mutuwar nasa kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona
Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya reshen jihar Taraba ya rasu sakamakon cutar korona Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Har zuwa mutuwarsa, Peter Gambo ya kasance shugaban kungiyar NLC reshen jihar Taraba inda yake a zangonsa na biyu.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai yi nasara a yaki da rashawa - Fadar shugaban kasa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, matarsa da diyarsa da suka kamu da cutar korona duk sun warke.

Ya bayyana hakan ne a wata takarda da ya fitar a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

"Mata ta, diyata da ni kaina duk mun warke daga cutar korona. Ba mu kadai ba, har da sauran iyalina da suka kamu da muguwar cutar.

"Muna godiya ga Ubangiji kuma muna mika sakon godiya ga duk wadanda suka taimaka mana da addu'a," ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Gwamnan Okowa yayi wannan sanarwar ne a sahihin shafinsa na Twitter.

Ya sanar da lokacin da suka kamu da muguwar cutar tare da bayyana cewa sun killace kansu.

Hakan ya faru ne bayan daya daga cikin 'ya'yan shi mata ta harbu da muguwar cutar numfashin.

A halin da ake ciki, kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta bayyana a ranar 14 ga watan Yullin 2020, sabbin mutum 463 sun sake harbuwa da cutar korona.

Lagos-128

Kwara-92

Enugu-39

Delta-33

Edo-29

Plateau-28

Kaduna-23

Oyo-15

Ogun-14

Osun-14

FCT-12

Ondo-9

Rivers-9

Abia-8

Bayelsa-5

Ekiti-3

Borno-2

Jimillar wadanda suka kamu da cutar sun kai 33,616 a Najeriya. An sallama 13,792 bayan warkewa garas daga jinyar cutar. Mutum 754 sun riga mu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel