"Satifket ya hana Segun Abraham shiga takarar Gwamnan Jihar Ondo a APC"

"Satifket ya hana Segun Abraham shiga takarar Gwamnan Jihar Ondo a APC"

Kwamitin tantance ‘yan takara a zaben jihar Ondo ta cire Segun Abraham, ‘dan a-mutun jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, daga cikin wadanda za su nemi takara.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto cewa wata matsala da aka samu game da satifket din karatun Segun Abraham ta sa aka hana sa shiga takarar Gwamna a jam’iyyar APC

A makon jiya kwamitin Tijani Tumsa ya bayyana cewa akwai wanda bai samu shiga cikin wadanda za su fafata a zaben fitar da gwanin APC wajen neman tikitin gwamnan Ondo ba.

Wannan mataki da kwamitin tsaida ‘yan takara na jam’iyyar APC ya dauka ya bada mamaki ganin Abraham ya na cikin ‘yan takarar da za su iya kawowa gwamna mai-ci matsala.

Tijani Tumsa da ‘yan kwamitinsa ba su bayyana cikakken dalilin cire Abraham daga cikin jerin mutane 12 da za su yi harin tikitin jam’iyyar APC a zaben na gwamnan jihar Ondo ba.

Jaridar ta samu bayani daga wata majiya mai karfi cewa Segun Abraham ya gaza gabatar da takardar digirinsa ne a gaban kwamitin, wannan ya sa aka hana sa shiga neman takara.

KU KARANTA: Jerin 'Yan takarar da ke harin kujerar Rotimi Akeredolu a APC

"Satifket ya hana Segun Abraham shiga takarar Gwamnan Jihar Ondo a APC"
Segun Abraham
Asali: Twitter

“Ba mu bayyana sunansa ba ne saboda ya na da damar daukaka matakin da mu ka dauka wajen tantancewar. Kwamitin sauraron korafi ne zai yanke hukuncin karshe a kan lamarin.”

Majiyar ta yi wa ‘yan jarida karin haske ba tare da an kama suna ba.

Ya ce rashin takardar digiri ta hana a sa Abrahama cikin ‘yan takarar APC a jihar Ondo, ba wai alakarsa da babban ‘dan siyasar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ba.

“Ya gabatar da shaidar kammala sakndare, amma ya fada mana cewa satifiket dinsa na digiri ya na kasar waje, to a kan wannan ne aka cire shi daga cikin ‘yan takara a APC.”

A halin yanzu ana sa ran cewa za a shirya zaben fitar da gwani a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli, 2020 ne. A nan ne za a sa wanda zai rikewa APC tuta a zaben gwamnan Ondo.

A zaben 2016, tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu ya marawa Abraham baya a zaben tsaida gwani, a karshe ya sha kashi a hannun Rotimi Akeredolu da kuri’u 34.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng