Yanzu Yanzu: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu

Yanzu Yanzu: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu

- Rundunar sojin sama ta sanar da mutuwar matukiyar jirgin yaki mace ta farko a Najeriya, Tolulope Arotile

- Arotile ta mutu a Kaduna a ranar Talata bayan ta ji wasu raunuka a kai sakamakon hatsarin mota, ta mutu tana da shekaru 23 a duniya

- An kaddamar da sojar a matsayin matukiyar jirgin yakin sojin saman Najeriya mace ta farko a ranar 15 ga watan Oktoba, 2019

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta sanar da mummunan labari na mutuwar matukiyar jirgin yakinta mace ta farko, Tolulope Arotile, wacce ta mutu watanni takwas bayan an yi mata karramawa ta musamman.

NAF ce ta sanar da labarin mutuwar Arotile, wanda aka bayyana a matsayin abun “takaici” a cikin wani jawabi a ranar Talata, 14 ga watan Yuli.

An tattaro cewa marigayiyar sojar ta rasu ne sakamakon hatsarin mota a Kaduna.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan fashi sun sanar da Jama'a da Ma’aikatan banki game da shirin hari a jihar Ebonyi

Matashiyar mai shekaru 23 a duniya ta amsa kiran mahaliccinta bayan ta ji wasu raunuka a kai sanadiyar hartsarin da ya afku a sansanin NAF dake Kaduna.

"Cike da tarin nauyin zuciya rundunar sojin saman Najeriya na bakin cikin sanar da mutuwar matukiyar jirginta Tolulope Arotile, wacce ta mutu a ranar 14 ga watan Yuli 2020, sakamakon raunukan da ta samu a kai daga hatsarin mota a sansanin sojin sama a Kaduna.

Yanzu Yanzu: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu
Yanzu Yanzu: Matukiyar jirgin yakin Najeriya mace ta farko ta rasu Hoto: NAF
Asali: Twitter

"Har zuwa mutuwarta, Fg Offr Arotile, wacce aka kaddamar cikin NAF a watan Satumban 2017 a matsayin mamba na makarantar tsaron Najeriya wato Nigeria Defence Academy RC 64, ta kasance matukiyar jirgin yaki ta farko a hukumar," cewar wani bangare na jawabin.

Yayinda take bayyana marigayiyar a matsayin rashi da ba za a samu madadinta ba, NAF ta mika ta'aziyya ga ahalin marigayiyar tare da addu'an Allah ya ji kanta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: An bi mamallakin kamfani GoKada an kashe har gida

An karrama Arotile tare da jami'ar sama Kafayat Sanni. matan biyu sun kasance cikin jerin matukan jirgin NAF 13 wadanda suka kammala atisayensu na tashi a kasar waje.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng