"30% na mutanen Garin Batsari sun zama ‘Yan gudun hijira saboda rashin tsaro"

"30% na mutanen Garin Batsari sun zama ‘Yan gudun hijira saboda rashin tsaro"

Mai martaba Hakimin Batsari, Sarkin Ruman Katsina, Tukur Mu'azu Ruma ya yi magana da BBC Hausa, inda ya bayyana irin mummunan halin da Bayin Allah su ke ciki a a kasarsa.

Alhaji Tukur Mu'azu Ruma ya shaidawa ‘yan jarida cewa yanzu haka su na da marayu fiye da 2, 000 a sakamakon kashe-kashen da ‘yan bindiga su ka yi a yankin.

A dalilin rashin tsaron da ya aukawa karamar hukumar Batsari, akalla mata 600 ne ake tunanin su na takaba bayan ‘yan bindiga sun raba su da mazajensu har abada.

Hakimin Batsari, Tukur Mu'azu Ruma ya kuma bayyanawa jaridar cewa kimanin mutum daya cikin uku da ake da su a kasarsa, sun koma gufun hijira a wasu bangarorin Najeriya.

A hirar makon nan, Sarkin Ruman Katsina ya ke cewa a halin yanzu, kusan babu wata rana ta Allah da wadannan ‘yan bindiga ba za su kai masu hari, su hallaka mutane ba.

Mai martaban ya ce an tarwatsa mutanensa duk sun tsere, bayan ga makukun asara da aka yi na dukiyar kayan abinci da dabbobi da dai makamantansu.

KU KARANTA: An kama wadanda su ka yi zanga-zanga saboda rashin tsaro a Katsina

"30% na mutanen Garin Batsari sun zama ‘Yan gudun hijira saboda rashin tsaro"
Wasu 'Yan IDP a Katsina Hoto: Facebook
Asali: Twitter

Wannan hare-hare da ake kai wa na babu gaira babu dalili, sun gurgunta tattalin arziki ta jawo karyewar harkar gona da kiwon dabbobi da sha’anin kasuwanci.

A shekarar da ta gabata, Hakimin ya ce kimanin 40% na moman yankin ba su yi noma ba. Bisa dukkan alamu lamarin ba zai gaza kai na bara kamari a yanzu ba.

Uban kasar ya roki gwamnati ta kawowa mutanen na sa dauki, duk da ya bayyana cewa ana ciyar da wadanda su ke fake bayan an raba su da gidajensu.

Kawo yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro a wannan kauye da wasu kananan hukumomi da-dama da ke cikin jihar Katsina.

Gwamnati ta yi alkawarin kawo karshen kashe-kashen da ake yi, a dalilin haka ta bada umarnin tura dakarun sojoji domin ganin bayan wadannan miyagu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel