Sojoji sun saki wasu ‘Yan kungiyar Boko Haram 602 da su ka tuba a Najeriya

Sojoji sun saki wasu ‘Yan kungiyar Boko Haram 602 da su ka tuba a Najeriya

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, wasu tsofaffin ‘yan Boko Haram 600 su ka samu ‘yanci a Najeriya bayan sun tuba daga mummunan aikin da su ke yi.

Wadannan sojoji sun rabu da ta’addanci, sun tuba, sannan kuma sun shiga wani tsari da aka tanada domin sake rikidar da su da canza masu tunani.

Bayan kammala wannan shiri, tsofaffin ‘yan ta’addan sun rantse ba za su sake komawa cikin irin wannan danyen aiki na hallaka Bayin Allah da sunan addini ba.

Mai magana da yawun bakin dakarun sojojin kasa na Operation Safe Corridor, Manjo-Janar Bamidele Shafa ya ce tsofaffin ‘yan ta’addan sun yi rantsuwar biyayya ga gwamnati.

Bamidele Shafa ya shaidawa ‘yan jarida cewa wadannan mutane ba za su sake shiga Boko Haram ba. A baya ma an saki mayaka 1, 400 wadanda su ka fice daga Boko Haram.

Yanzu haka kuma akwai wasu ‘yan ta’adda 280 wadanda su ka nuna sha’awar fita daga kungiyar, su ma su na tsare a wannan cibiya ta rikida tunanin tsofaffin ‘yan ta’addan.

KU KARANTA: Hafsun Soji ba su kunyata 'Yan Najeriya da Buhari ba - Buratai

Sojoji sun saki wasu ‘Yan kungiyar Boko Haram 602 da su ka tuba a Najeriya
Hedikwatar gidan sojin kasa
Asali: Twitter

Jaridar Anadolou Agency ta ce an kama wadannan mayaka ne a yankin Borno, Adamawa da Yobe da ke Arewa maso gabas.

Kawo yanzu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 30, 000. Bayan haka daga 2009 zuwa yanzu, sun fatattaki mutane miliyan uku daga gidajensu.

Tsofaffin 'yan ta’addan sun bayyana gaban wani zaure inda su ka amsa laifuffukan da su ka yi a baya, su ka sanar da cewa sun bar Boko Haram, kuma su ka yi sabuwar rantsuwa.

Janar Bamidele Shafa ya bayyana cewa wadannan mayaka sun yi rantsuwar yin biyayya da bin umarnin gwamnatin tarayyar Najeriya sau-da-kafa.

Janar Shafa ya ce bayyanar wadannan mutane a gaban zauren ya nuna cewa lallai sun tuba.

Jiya mun ji cewa Boko Haram sun sace shugaban ‘yan sa-kai, wanda ya ke taimakawa sojoji a yakin Boko Haram a jihar Borno, Abdulkareem Umar wanda aka fi sani da Maigiwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel