Agu ya tafi kotu, ya na so a maida mutanen Oshiomhole kan kujerunsu a APC

Agu ya tafi kotu, ya na so a maida mutanen Oshiomhole kan kujerunsu a APC

- Wasu jiga-jigan APC su na kalubalantar ruguza majalisar NWC da aka yi kwanaki

- Buhari ya bada shawarar a janye karan da su ke kotu bayan an sauke shugabanni

- Akwai wadanda su ka yi uwar-shegu da wannan kiran da Shugaban kasar ya yi

Jaridar Leadership ta fitar da rahoto da ke nuna cewa abubuwa basu tafiya daidai a jam’iyyar APC duk da an nada sababbin shugabannin rikon kwarya.

Wasu manyan jam’iyyar mai mulki sun yi fatali da umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada a game da rikicin da ake fama da shi a APC na tsawon lokaci.

Shugaban kasa ya nemi a janye duk karar da ‘yan jam’iyya su ka shigar a gaban kotu a Najeriya.

Makonni kusan uku da yin taron NEC wanda aka dauki wannan mataki, Kalu Agu, ya dumfari kotu ya na kalubalantar matakin da majalisar kolin jam’iyyarsa ta dauka.

Barista Kalu Agu ya na neman a soke ruguza majalisar NWC ta Adams Oshiomhole da aka yi, ya ce yin hakan ya ci karo da kundin tsarin mulki.

Agu wanda jagoran matasan jam’iyyar APC ne a jihar Abia, bai gamsu cewa majalisar NEC ta na da ikon tsige shugabannin jam’iyya kafin su kammala wa’adinsu ba.

KU KARANTA: APC: Bangarorin Amaechi da Abe su na cigaba da rikici a Ribas

Agu ya tafi kotu, ya na so a maida mutanen Oshiomhole kan kujerunsu a APC
Taron NWC Hoto: Jam'iyyar APC
Asali: UGC

Shugaban matasan APC na jihar ta Abia ya ke cewa Adams Oshiomhole da sauran shugabannin da aka ruguza ba su cika shekaru biyu masu kyau a kan mulki ba.

Barista Kalu ya na neman babban kotun tarayya da ke Abuja ya dakatar da ruguza majalisar NWC, ya bayyana wannan mataki da cewa ya ci karo da doka, ya saba ka’ida kuma ba zai yi aiki ba.

Kafin karar Agu, Lateef Arigbaruwo wanda ya na cikin manyan APC a jihar Legas ya shigar da makamancin wannan kara a wani babban kotun da ke zama a Legas.

Shi ma Lateef Arigbaruwo ya na neman kotun ta sallami kwamitin Mai Mala Bunin na rikon kwarya da aka nada domin su jagoranci sabon zaben jam’iyya na kasa.

A kara mai lamba FHC/L/CS/789/2020, Lauyan Arigbaruwo ya na so a kyale Hilliard Eta ya jagoranci zaman NEC da NWC da duk sauran al’amuran jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel