Dangantaka ta da Buhari tamkar na uba da ‘da ne - Obaseki

Dangantaka ta da Buhari tamkar na uba da ‘da ne - Obaseki

- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya bayyana alakarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu

- Obaseki ya tabbatar da cewar akwai kyakyawar alaka irin ta uba da 'dansa a tsakaninsa da shugaban kasar

- Ya bayyana hakan ne bayan ganawar da ya yi da shugaban kasar ta manhar Zoom

Gwamnan jihar Edo mai ci kuma dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan jihar da za a yi a watan Satumba, Godwin Obaseki ya bayyana alakarsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu.

Obaseki ya tabbatar da cewar akwai kyakyawar alaka irin ta uba da 'dansa a tsakaninsa da shugaban kasar.

Gwamnan ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter inda ya ce sun gana da shugaban kasa Buhari ta manhajar Zoom.

KU KARANTA KUMA: Magu: Daraktocin EFCC sun hallara gaban kwamiti, an jero musu tuhumar da ake musu

Dangantaka ta da Buhari tamkar na uba da ‘da ne - Obaseki
Dangantaka ta da Buhari tamkar na uba da ‘da ne - Obaseki Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Ya kuma bayyana cewa sun tattauna lamuran da suka shafin ci gaban al'umman jihar Edo da na Najeriya baki daya.

Ya kara da cewar sun tattauna yadda za a shawo kan annobar Coronavirus.

Ya ce: "Alaka ta da shugaban kasa Muhammadu Buhari irin ta mahaifi da da ce.

"Mun yi taro ta manhajar Zoom da shugaban kasar. Mun tattauna a kan al'amuran ci gaba da suka shafi jama'ar jihar Edo da Najeriya baki daya.

"Mun tattauna yadda za a shawo kan annobar Coronavirus."

KU KARANTA KUMA: Magu ya yi martani a kan 'ribar' saman N550bn da ake zarginsa da kwashewa

A gefe guda mun ji cewa gwamnoni karkashin jam'iyyar APC sun fara neman wanda zai maye gurbin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.

Har zuwa lokacin da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP, Obaseki ne mataimakin shugaban zauren gwamnonin APC.

Jaridar New Telegraph ta ruwaito cewa ana cike wannan gurbin ne duba da yanki.

Kuma ana bai wa yankin Kudu ne saboda shugaban kungiyar, Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, dan arewa ne.

Jaridar ta bayyana cewa Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma ya nuna muradin maye wannan gurbin.

Yankin kudun maso gabas na APC sun fara neman goyon bayan sauran gwamnonin don nasarar Uzodinma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel