Gwamnati ta yi alkawari rage kudin waya a wajen taron horas da ‘yan jarida

Gwamnati ta yi alkawari rage kudin waya a wajen taron horas da ‘yan jarida

Ana sa ran cewa kudin da jama’a su ke kashewa wajen yin kira a wayar salula zai ragu da kashi 40% bayan matakan da gwamnatin tarayya ta dauka.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa za a ga ragi a kudin waya bayan sun kwadaito da masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.

Dr. Isa Ibrahim Pantami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta shawo kan kalubalen da ake samu na kudin jawo igiyoyin RoW, da kuma tsare kayan aiki.

Isa Ibrahim Pantami ya yi wannan jawabi ne a wajen bude bikin koyon aiki da hukumar NITDA ta shirya wanda za ayi tsawon mako guda ana yi a birnin tarayya Abuja.

Ministan kasar ya shaidawa jama’a cewa cigaban da su ka kawo wajen kayan aikin sadarwa ya sa kamfanoni sun samu damar ratsa 40.18% na jama’a, daga 30% a shekarar bara.

KU KARANTA: Pantami: Aljihuna ya fi nauyi kafin in zama Ministan Buhari

Gwamnati ta yi alkawari rage kudin waya a wajen taron horas da ‘yan jarida
Isa Pantami da wasu Ministoci a taro Hoto: FEC
Asali: Twitter

Hukumar NITDA wanda ta ke karkashin ma’aikatar sadarwa ta shirya wannan taro ne ga ‘yan jarida domin samun kwarewa a harkar sadarwa ta zamani.

Mai girma ministan ya ce gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta na harin yadda farashin yin waya da hawa yanar gizo zai karye da 40% daga yanzu zuwa shekarar 2025.

A cewarsa, matakam da su ke dauka ya na cikin tsare-tsaren gwamnatin tarayya mai-ci na inganta harkar sadarwar zamani da kuma ragewa jama’a radadin rayuwa.

Har ila yau, ministan ya kara da cewa gwamnati za ta bada karfi wajen kwarewa a aiki a maimakon takardun shaida da digiri, wanda yin hakan zai kawo ayyukan yi a kasa.

Wannan horo da za a ba ‘yan jarida zai taimaka masu wajen inganta kwarewarsu a wurin aiki.

A karshe, ministan ya yi kira ga ‘yan jaridar da za a ba horo, su maida hankali wurin kawo rahoton gaskiya da adalci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel