Kungiyar Mazauna Garin Batsari sun ce Sojoji ba su kashe ‘Yan bindiga ba

Kungiyar Mazauna Garin Batsari sun ce Sojoji ba su kashe ‘Yan bindiga ba

Kungiyar BALDF ta mazauna karamar hukumar Batsari, ta yi watsi da jawabin da dakarun sojojin Najeriya su ka yi na cewa sun kashe wasu ‘yan bindiga 46 a harin da su ka kai.

Sojojin Najeriya su na ikirarin sun kai harin gayya, inda su ka kashe ‘yan bindiga a Batsari.

Wasu daga cikin mazauna wannan gari da ke jihar Katsina ta bakin shugaban kungiyar BALDF, sun ce ba gaskiya dakarun sojojin kasar su ke fadawa Duniya ba.

A wani jawabi da Sani Muslim ya fitar a madadin BALDF, ya ce sojojin sun yaudari mutane da jawabin da su ka fitar, domin kuwa babu ‘dan bindiga ko guda da su ka kashe.

Malam Sani Muslim ya shaidawa PRNigeria cewa bayan ‘yan bindigan sun hallaka kauyawa 18 a harin da su ka kai, har su ka tattara su ka tafi, babu jami’in tsaron da ya kawo dauki.

Don haka ne Sani Muslim ya yi kira ga sojojin da ake fafatawa da su a fagen daga da su rika fadawa hedikwatar gidan sojan gaskiyar abin da ya ke faruwa dauke da hotuna da bidiyo.

KU KARANTA: Tsohon Soja ya bayyana abubuwan da su ka jawowa Magu matsala

Kungiyar Mazauna Garin Batsari sun ce Sojoji ba su kashe ‘Yan bindiga ba
Gwamnan Katsina Aminu Masari
Asali: UGC

“Mun godewa jami’an tsaro da su ke sadaukar da ransu domin ganin an samu zaman lafiya a karamar hukumar Batsari da jihar Katsina domin a cigaba da harkokin rayuwa.”

Muslim ya kara da cewa: “Sai dai duk da haka, sai an kara kokari sosai, musamman a bangaren samun bayanai da kai samame ga miyagun da su ka sa rayuwa ta ke neman ta gagare mu.”

Shi ma hakimim garin Batsari, Alhaji Mohammed Muazu, a wata hira da ya yi ‘yan jarida ya koka da yadda ‘yan bindiga su ke jefa tsoro a zukatan al’ummarsa.

Mai martaban ya ke cewa: “Mutane ba za su iya zuwa gonakinsu ba saboda gudun hare-hare. Har a cikin manyan garuruwa da kauyukan masarautar, mutane ba su iya barci da minshari.”

Janar John Enenche a wani jawabi da ya fitar a makon da ya gabata, ya ce dakarun Super Camp 4 sun hallaka ‘yan bindiga kusan 50 a kauyen ‘Yar gamji da ke cikin garin Batsari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel