Ma su garkuwa da mutane sun sace tsohon sanatan arewa

Ma su garkuwa da mutane sun sace tsohon sanatan arewa

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Taraba ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon mamba a majalisar dattijai, Sanata Zik Sunday.

Sanata Sunday ya wakilci sanatoriyar Taraba ta kudu a majalisar dattijai daga shekarar 2003 zuwa 2007.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Taraba (PPRO), DSP David Misal, ya tabbatar da faruwar sace Sanata David ga manema labarai a Jalingo.

DSP Misal ya bayyana cewa an sace Sanatan ne a gidansa da ke karamar hukuma Karim Lamido, amma ana kokarin kubutar da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandar ya sake bayyana cewa gungun wasu 'yan bindiga sun sace babban limamin masallacin ofishin rundunar 'yan sanda, Mustapha Badamasi, jami'an dan sanda mai mukamin kofural.

Ya ce an sace Badamasi a gidansa da ke unguwar Sabongari a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Misal ya bawa iayalan mutanen da aka sace tabbacin cewa rundunnar 'yan sanda za ta yi iyakar bakin kokarinta wajen kubutar dasu tare da kama wadanda su ka yi garkuwa dasu.

Ma su garkuwa da mutane sun sace tsohon sanatan arewa
Sanata Zik Sunday
Asali: UGC

A wani labarin mai nasaba da wannan da Legit.ng ta wallafa, 'yan bindiga sun sace babban limamin rundunar 'yan sandan jihar Taraba, Mallam Mustapha Nuhu.

DUBA WANNAN: Yadda na yaki cin hanci, na tarawa Najeriya makudan biliyoyi - Ngozi Okonjo-Iweala

An yi garkuwa da babban dan sandan ne a daren ranar Lahadi, 12 ga watan Yuli, kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

'Yan bindiga, da za su kai 10, sun tsinkayi gidan Malamin da ke kwatas din Nana Aisha a tsakar dare tare da sace shi.

Malamin, kuma babban dan sanda, ya na aiki da rundunar 'yan sandan jihar Taraba.

An gano cewa yayi wa'azi a kan yawaitar laifuka musamman garkuwa da mutane a jihar Taraba yayin hudubar Sallar Juma'a.

A lokacin rubuta wannan rahoton, masu garkuwa da mutanen basu tuntubi iyalan dan sandan ba.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, 'yan bindiga na ta kai hari a tsakiyar birnin Jalingo a cikin makonnin baya bayan nan.

An gano cewa, unguwannin da abun yafi shafa sun hada da kusa da gadar Donga, Baba Yau, Mile 6, Kona, Wuro Sambe, Sabongari da yankin firamare.

An gano cewa mazaunan yankin na cike da tsoro tare da fargabar masu garkuwa da mutanen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel