Nnamani. Ngige sun fara yunkurin tallata APC da Buhari a kasar Inyamurai

Nnamani. Ngige sun fara yunkurin tallata APC da Buhari a kasar Inyamurai

A karshen makon nan ne wasu manyan jagororin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso gabashin Najeriya su ka yi wani zama na musamman a gidan gwamnatin jihar Imo.

Ministoci biyar da ke gwamnatin shugaban kasa Muhammadu, Sanata Dr. Ken Namanni, da gwamna Hope Uzodimma sun shirya wannan taro ne domin harin siyasar 2023.

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa an yi wannan zama ne ranar Lahadi a garin Owerri, jihar Imo.

Makasudin zaman shi ne yadda ‘yan siyasar za su shiryawa 2023, sannan kuma su ka fitar da matsaya cewa za su ba gwamnatin Muhammadu Buhari goyon-baya.

‘Yan siyasar sun nuna cewa marawa Muhammadu Buhari baya zai taimakawa mutanen Kudu maso gabashin kasar cin romon gwamnatin APC mai-ci.

Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma ya yi wa ‘yan jarida bayani bayan an kammala taron inda ya shaidawa Duniya makusudin wannan zama da su ka yi daga su sai su.

KU KARANTA: Magoya bayan jiga-jigan APC sun sake barke da rikici a Ribas

Nnamani. Ngige sun fara yunkurin tallata APC da Buhari a kasar Inyamurai
Sanaya Hope Uzodinma Hoto: Aso Villa
Asali: Facebook

Hope Uzodimma ya ce a shirya su ke da su hada-kai da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin yankin kasar su ci moriyar gwamnatin tarayya.

Ministocin da su ka halarci taron sun hada da na ilmi, kwadago, fasaha, albarkatu, da na kasar waje; Emeka Nwajiuba, Chris Ngige; Ogbonaya Onu, Uche Uga, Minister da Geoffery Onyeama.

Uzodinma ya shaidawa manema labarai cewa za su dage wajen ganin sun karfafa APC a bangaren kasar ta yadda jam’iyyar za ta yi farin jini a wajen mutanen Ibo.

Makasudin zaman shi ne ganin yadda za a budewa jihohin Kudu maso gabas biyar dama a gwamnatin tarayya inji gwamnan na APC.

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ken Nnamani ya ce manyan jam'iyyar sun shirya wannan taro a Imo ne domin ita kadai ce jihar da APC ta ke mulki a yankin.

Bayan Ken Nnamani, Dr. Chris Ngige ya yi jawabi, ya ce wadanda su ke cikin gwamnatin Buhari za su yi kokarin kawowa Ibo ayyukan gwamnatin tarayya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng