Yaran Rotimi Amaechi da Magnus Abe su na fada a kan kiran a rufe ofisoshin APC

Yaran Rotimi Amaechi da Magnus Abe su na fada a kan kiran a rufe ofisoshin APC

Magoya bayan ministan sufuri, Rt. Hon. Rotimi Amaechi, da yaran Magnus Abe sun sake barkewa da rikici a jihar Ribas.

Jaridar The Punch ta ce abin da ya haddasa rikicin shi ne kiran da Igo Aguma ya yi na cewa a rufe duk wata sakatariya ta ‘yan tawaren APC a jihar Ribas.

Wannan rigima da ake yi ta zo daidai lokacin da jam’iyyar APC ta ke kokarin dinke barakar da cikin gidanta bayan an nada sababbin shugabannin rikon kwarya.

A ranar Asabar ne Igo Aguma wanda kotu ta tsaida a matsayin ainihin shugaban APC ne Ribas, ya bada umarnin a rufe ofisoshin ‘yan taware a fadin jihar.

Aguma ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan ya tuntubi kwamitin Mai Bala Buni wanda aka ba alhakin tafiyar da jam’iyyar kafin a shirya zaben shugabanni.

A jawabin da shugaban jam’iyyar ta APC ya fitar ta bakin hadiminsa Livingston Nwechie, ya yi kira ga Dr. Sokonte Davies ya janye kayan yakinsa.

KU KARANTA: Akwai hannun Amaechi da Gwamnonin APC a rikicin Ondo

Yaran Rotimi Amaechi da Magnus Abe su na fada a kan kiran a rufe ofisoshin APC
Rotimi Amaechi da Magnus
Asali: Depositphotos

APC ta na zargin cewa Sokonte Davies da magoya bayansa su na cikin masu kawowa jam’iyyar matsala a Ribas, don haka aka bukaci su rufe ofishin da su ke aiki.

Wannan mataki da Igo Aguma ya dauka bai yi wa bangaren Rrotimi Amaechi dadi ba, wanda su kuma ba su ga maciji da Sanata Magnus Abe.

Tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi ya na cikin manyan APC. Shi kuma Magnus Abe wanda ya rike kujerar Sanata zuwa 2019 ya na cikin ‘yan adawar Ministan a cikin-gida.

Sakataren yada labarai na APC a Ribas, Ogbonna Nwuke, ya maidawa bangaren Igo Aguma martani, ya na sukar matakin da su ka dauka na cewa a rufe sauran ofisoshin jam’iyya.

Ogbonna Nwuke wanda ake zargin yaron Rotimi Amaechi ne, ya bayyana cewa an dakatar da Aguma daga jam’iyyar APC a jihar Ribas tun ba yau ba.

Kakakin na APC ya ce don haka, tun farko Aguma bai da hurumin da zai fito ya na bada umarnin korar shugabannin APC daga sakatariyar jam’iyya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel