Magu: Daraktocin EFCC sun hallara gaban kwamiti, an jero musu tuhumar da ake musu

Magu: Daraktocin EFCC sun hallara gaban kwamiti, an jero musu tuhumar da ake musu

- Daraktocin hukumar yaki da rashawa sun hallara a gaban kwamitin da ke bincikar dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu

- Sun bayyana gaban kwamitin ne domin amsa wasu tambayoyi

- An dai dakatar da Magu a makon da ya gabata tun bayan fara fuskantar kwamitin bincikensa da yayi a fadar shugaban kasa

Wasu daraktocin hukumar yaki da rashawa (EFCC), na fuskantar kwamitin yaki da rashawa da aka kafa don bincikar dakataccen shugaban hukumar, Ibrahim Magu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Magu a makon da ya gabata tun bayan fara fuskantar kwamitin bincikensa da yayi a fadar shugaban kasa.

A ranar Litinin da ta gabata ne aka kama Magu tare da tisa keyarsa har fadar shugaban kasa inda yake amsa tambayoyi a kan yadda ya jagoranci hukumar.

Magu: Daraktocin EFCC sun hallara gaban kwamiti, an jero musu tuhumar da ake musu
Magu: Daraktocin EFCC sun hallara gaban kwamiti, an jero musu tuhumar da ake musu Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Banda ranakun Asabar da Lahadi, Magu ya bayyana a gaban kwamitin da ya samu shugabancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara a kowacce rana.

Kwamitin ya fara zamansa tun makonni uku da suka gabata amma bai kira Magu ba har sai makon da ya gabata.

Tun bayan tsaresa, an umarci Umar Mohammed wanda shine daraktan ayyuka da ya karbi ragamar hukumar.

A ranar Alhamis, kwamitin ya tuhumi wata kungiya da ake kira da "Magu Boys" wadanda ake zargin suna wa Magu aiki.

KU KARANTA KUMA: Binciken badakalar EFCC: Magu ya sake bayyana gaban kwamiti

Ana zargin su da abubuwa masu tarin yawa da suka hada da bata suna, karbar rashawa daga wadanda ake zargi tare da siyar da kadarorin da aka kwace ga wadanda suke so ba tare da zuba wa gwamnati kudin ba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ana zargin Ibrahim Magu, da mayar da EFCC tamkar ofishin 'yan sanda saboda wani ra'ayi nashi na kanshi.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya sanar, wannan na kunshe ne a rahoton kwamitin kula da yadda aka samo dukiyoyin da aka wawure na fadar shugaban kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin don ya duba al'amuran EFCC karkashin jagorancin Magu.

ranar Juma'a da ta gabata ne sifeta janar din 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bada umarnin janye 'yan sandan da ke tsaron lafiyar Magu wanda aka tsare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel