Yadda Buhari ya bai wa DSS umarnin bincikar Magu tun 2018
A rashin sanin Ibrahim Magu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar jami'an tsaro ta farin kaya da ta bincikesa tun a 2018, jaridar The Cable ta ruwaito.
DSS ce ta yi babban aiki wurin bankado duk zargin da ake wa dakataccen shugaban hukumar EFCC wanda a yanzu fadar shugaban kasa ke bincikarsa.
An gano cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya matukar girgiza bayan da jami'an DSS suka kawo gamsassun bayanai a kan harkallar kudade da Magu ke yi.
"Idan da a ce Magu na karantar alamu, da ya gane cewa shugaban kasa bai mika sunansa gaban majalisa ba don tabbatar da shi tun bayan kafa sabuwar majalisar tarayya," wata majiya mai karfi daga fadar shugaban kasa ta sanar da The Cable.
Majalisar tarayyar yanzu bata taba kin aminta da wani nadin da shugaban kasa yayi ba kamar yadda tsohuwar majalisar tarayya ta ki aminta da Magu.
"Ya zo masallacin fadar shugaban kasa don yin sallar Juma'a a ranar 5 ga watan Yuni, amma sai shugaban kasa ya ki sakin jiki da shi," majiya ta sanar.
"Shugaban kasar ya fi son yin sallah da iyalansa tare da hadimansa. Don haka ne bai yi farin cikin ganin Magu a masallacin ba duk da an dage dokar kulle.
"Daga nan aka bada umarnin cewa kada a sake barinsa zuwa masallacin."
Abinda ya assasa binciken hukumar DSS kuwa kamar yadda majiyar tace, shine rahoton kwamitin fadar shugaban kasar na dukiyoyin da aka samo.
Kwamitin na da mutum 3 a cikinsa kuma an rantsar da su a ranar 22 ga watan Nuwamban 2017, don bada bayanin dukiyar da aka samo tun daga ranar 29 ga watan Mayun 2015.
Olufemi Lijadu, Mohammed Nami da Gloria Bibigha ne mambobin kwamitin.
KU KARANTA KUMA: Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai
A halin yanzu Lijadu ne shugaban SEC yayin da Nami ya zamo shugaban FIRS. Bibigha na aiki a ofishin odita janar na tarayya.
Kwamitin ya mika rahotansa a watanni shida da suka gabata kuma al'amarin EFCC ya bai wa shugaban kasar mamaki matuka. A nan ne Buhari ya bukaci a bincike Magu.
A yayin da DSS ta gano wasu kadarori wadanda Magu ya mallaka a Dubai, NFIU ta taka rawar gani wurin baya bayanan sirri a kan harkallar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng