Rundunar soji ta yi karin bayani a kan barin aikin dakaru 365

Rundunar soji ta yi karin bayani a kan barin aikin dakaru 365

Rundunar sojin Najeriya ta musanta rahoton cewa dakarunta 365 sun yi murabus ne saboda sun gaji da aikin soja.

A cewar rundunar soji, dakarun sun bar aiki ne saboda sun cika ka'idar yin ritaya bayan sun shafe shekaru 35 su na aiki.

Jaridar 'The Nation' ta wallafa cewa majiyarta a rundunar soji, wacce ta nemi a boye sunanta, ta sanar da ita cewa an aikawa dukkan sojojin takardar sanarwar lokacin yin ritayarsu amma sai wasu su ka yi sakaci ta shiga hannun kafafen yada labai.

A cewar 'The Nation', majiyarta ta nemi a boye sunanta ne saboda rundunar soji ta yanke shawarar cewa ba za ta fitar da wata sanarwa dangane da rahoton da kafafen watsa labari su ka wallafa ba.

Majiyar ta sanar da 'The Nation' cewa ba bakon abu bane a samu sojoji da yawa sun yi ritaya daga aiki kuma an maye gurbinsu kowacce shekara.

Ya kara da cewa dukkan sojojin 365 za su tafi zuwa wata cibiyar soji ta musamman domin ba su horo a kan sana'o'in dogaro da kai bayan ritaya daga aiki.

"Abu ne da rundunar soji ta saba yi duk shekara, ta sallami jami'an da su ka shafe shekaru 35 su na aiki.

"Ana sanar da su wata uku kafin lokacin ritayarsu, inda za a basu horo a kan dabaru da sana'o'in dogaro da kai na tsawon wadannan watanni uku a wata cibiyar rundnar soji ta musamman da ke jihar Legas.

"Sakon sanarwar da aka aikawa sojojin ne ya fada hannun wasu masharrantar 'yan jarida su kuma suke wallafa cewa sojojin sun yi murabus ne saboda sun gaji da aiki," a cewar majiyar.

Majiyar ta bayyana cewa ba laifi bane a sallami mutum daga aiki bayan karewar wa'adin shekarun aikinsa da kundin tsarin mulki ya tanada.

Rundunar soji ta yi karin bayani a kan barin aikin dakaru 365
Janar Tukur Buratai, babban hafsan rundunar soji
Asali: UGC

Rahoto daga Premium Times ya nuna cewa da yawa cikin Sojojin da sukayi murabus daga aikin Soja sun kasance wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa maso gabashin Najeriya.

Akwai wasu kuma dake aiki a wasu yankunan daban.

A yanzu dai hukumar Sojin Najeriya na fuskantar barazana a dukkan yankunan Arewacin Najeriya.

DUBA WANNAN: Ondo: APC ta yi watsi da takarar na hannun daman Tinubu

Yayinda ake fama da yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso gabas, ana fama da yan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa maso yamma, sannan rikicin makiyaya da manoma a tsakiya.

Amma sabanin Soji 356 da sukayi murabus sakamakon gajiya da aiki, wasu 24 daban sun yi ritaya saboda son karbar sarauta a kauyukansu, jimillan Soji 380 kenan, majiyar PT ta bayyana.

Wata majiya daban tace banda wadanda ke murabus daga aikin Soja bisa tsari, Sojoji da dama sun gudu daga aikin musamman wadanda ke yakin Boko Haram a Arewa masio gabas, cewar majiya dake fagen fama.

Za ku tuna cewa a lokuta da dama kwamandoji da Sojoji sun bayyana a bidiyo suna kuka kan rashin isassun kayayyakin aiki da makamai domin yakar yan ta'addan Boko Haram.

Misalin haka shine lokacin da tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Olusegun Adeniyi, ya bayyana cikin wani bidiyo yana bayanin yadda yan Boko Haram sun fi su yawan makami.

Ba tare da bata lokaci ba aka tsoge Olusegun Adeniyi kuma aka maye gurbinsa da Farouq Yahaya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng