Jarumar fina-finan Indiya, Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar korona

Jarumar fina-finan Indiya, Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar korona

- Fitacciyar Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar coronavirus

- Hakan ya biyo bayan kamuwar da cutar da sirikinta Amitabh Bachchan da mijinta Abhishek suka yi

- Sai dai ba a sani ba ko suma an kwantar da su a asibiti kamar yadda aka kwantar da Amitabh da mijin nata a ranar Asabar

- Amitabh Bachchan dai ya yi kira ga makusantansa da su garzaya don yin gwajin cutar tun bayan da aka tabbatar da yana dauke da ita

Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Indiya wato Bollywood, Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar coronavirus.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan sirikinta Amitabh Bachchan da mijinta Abhishek sun kamu da annobar ta korona.

Ministan lafiya na kasar Indiya, Rajesh Tope ne ya wallafa hakan a twitter inda ya tabbatar da cewa Aishwarya da 'yarta sun kamu da wannan cuta.

Jarumar fina-finan Indiya, Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar korona
Jarumar fina-finan Indiya, Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta sun kamu da cutar korona Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Sai dai ba a sani ba ko suma an kwantar da su a asibiti kamar yadda aka kwantar da Amitabh da mijin nata a ranar Asabar, shashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Masu dauke da cutar a Indiya sun kai 850,000 ya yin da aka bayyana kamuwar mutum sama da 28,000 da suka kamu cikin awa 24.

KU KARANTA KUMA: Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai

A baya mun ji cewa fitaccen jarumin masana'antar Bollywood, wanda ya yi suna a duniya, Amitabh Bachchan, ya kamu da muguwar annobar nan da ta game duniya tare da zama ruwan dare.

Jarumin mai shekaru 77 ya kamu da cutar kuma an kwantar da shi a asibiti a ranar Asabar a garinsu na Mumbai.

Ya yi kira ga makusantansa da su garzaya don yin gwaji, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

"Na kamu da cutar korona kuma an mika ni asibiti," Bachchan ya rubuta yayin da yake sanar da cewa an yi wa iyalansa da hadimansa gwaji amma suna jiran sakamako.

"Duk wadanda suka kusanceni a kwanaki 10 da suka gabata, ina kira garesu da su garzaya don gwaji!" ya kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel