Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai

Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai

Kwamitin fadar shugaban kasa a kan bayanin kadarorin da aka samo (PCARA) ya ce Ibrahim Magu, dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa (EFCC), ya yi amfani da wani malamin addini wajen watanda da kudade a kasashen ketare.

A halin yanzu, ana tuhumar Magu a gaban wani kwamiti wanda yake samun shugabancin Ayo Salami, tsohon shugaban kotun daukaka kara.

An zargesa da rashin bayani a kan dukiyoyin da hukumar ke kwacewa a hannun mahandama.

A wani rahoton PCARA, gwamnatin tarayya ta gano cewa tsakanin watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2020, hukumar tayi amfani da wani fasto mai suna Emmanuel Omale, wurin sake handame kudaden hukumar.

An bankado sunan Omale yayin wani binciken ayyukan EFCC da NFIU tayi.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, faston ya siya wata kadara ta miliyan N573 a Dubai da ke daular larabawa a madadin Magu.

Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai
Rahoto: Yadda Magu yayi amfani da wani fasto ya siya kadara a Dubai Hoto: The Cable
Asali: UGC

"Wani mutum da ke taimakawa mukaddashin shugaban EFCC wurin sake watanda da kudin mai suna Emmanuel Omale ya bayyana," rahoton ya sanar.

"An gano cewa ya tafi har Dubai tare da Magu kuma sunansa aka saka wurin siyan kadarar wacce mallakin Magu ce.

"NFIU ta bankado fitar wasu kudi har N573,228,040.41 zuwa wani fasto da ba a sani ba."

Rahoton ya shafi tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke.

PCARA ya zargi Magu da kin hada kai da hukumomi a Ingila wurin tuhumarta yadda ya dace.

"A tuhumar Diezani Alison Madueke, mukaddashin shugaban EFCC ya kasa hada kai da NCA ta ingila wacce za ta bashi damar gurfanar da tsohuwar ministar a gaban Kotun Ingila," rahoton yace.

"Duk da sanin da yayi cewa ba za a iya dawo da Madueke Najeriya ba har sai an fara gurfanar da ita a gaban kotu a Ingila, ya ci gaba da zargin gwamnatin Ingila da hana kawo ministar Najeriya."

An zargi Magu da kin fitar da shaidu a rubuce da za su bai wa ofishin Antoni janar din Najeriya damar dawo da Diezani gida Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Buhari ya yi magana a kan tuhuma da dakatar da Magu

"Wannan al'amarin ya bata dangantarkar EFCC da Turai," rahoton yace.

Magu, wanda ke hannun 'yan sanda a Abuja, ana tsammanin zai sake bayyana gaban kwamitin bincike na Salami a ranar Litinin don kare kansa a kan zargin da ake masa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel