Baka bayar da beli ranar Juma’a ba amma kana so a baka beli ran Juma’a - Shehu Sani ya caccaki Magu

Baka bayar da beli ranar Juma’a ba amma kana so a baka beli ran Juma’a - Shehu Sani ya caccaki Magu

- Shehu Sani ya caccaki Ibrahim Magu kan halin da yake ciki

- Magu na fuskantar tuhuma kan zargin rashawa

- Tsohon sanatan ya ce giyar mulki a matsayin shugaban EFCC na ta jefa Magu cikin maye

Tsohon dan majalisar dokokin tarayya, Shehu Sani, ya sake caccakar dakataccen mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu.

Legit.ng ta rahoto cewa tsohon sanatan a wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli, ya ce mayen shugabancin EFCC na ta dibar Magu.

Magu, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin cin hanci, na tsare tun a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Sani ya bayyana cewa mafi akasarin maza a gurbin mulki kan manta da cewar mulki mai shudewa ne kuma yana zuwa da illoli.

Ya wallafa a Twitter: “A duk lokacin da ka tunatar da masu mayen mulki cewa mulki mai karewa ne kuma yana zuwa da illoli, sai su ga kamar ba zai taba faruwa a kansu ba.”

Tsohon dan majalisar ya yi mamakin dalilin da ya sa Magu wanda ya gaza bayar da beli ranar Juma’a a lokuta da dama ke rokon kwamitin shugaban kasa da ya bashi beli a yanzu.

“Mutumin da ya ke kin bayar da beli a ranar Juma’a ne ke son a bashi beli a ranar Juma’a; yana son karban abunda shi ba zai iya bayarwa ba,” in ji shi.

KU KARANTA KUMA: An kama wasu mutum 12 da ake zargi da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Niger

Sani ya bayyana cewa fursunonin kurkuku basu girmama manyan mutane.

Abu na farko da fursunoni za su fada maka idan ka shiga kurkuku shine “kai mallam nan kurkuku ne, muna da namu shugabancin a nan, kada ka zo kana babban mutum a nan, idan baka so mu dagargaza ka a nan toh ka bi a sannu da kuma biyayya a nan, ka ji ko?” ya wallafa.

A gefe guda, Ayodele Fayose, ya yi ikirarin cewa dakataccen mukadashin shugaban hukumar yaki da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu ya rika sayarwa abokansa kadarorin da ya ke kwato wa.

A cewar tsohon gwamnan na jami'yyar PDP, cikin wadanda Magu ke sayarwa kadarorin na gwamnati har da wasu lauyoyi masu rajin kare hakkin bil adama.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng