An kashe kwamandoji 8 da 'yan bindiga ma su yawa a jihar Zamfara
Dakarun rundunar sojin sama (NAF) a karkashin atisayen HADARIN DAJI sun kashe kwamandoji 8 tare da wasu dumbin sauran 'yan bindiga yayin wani luguden wuta da su ka yi a dajin Kagara.
Manjo Janar John Enenche, shugaban sashen yada labaran atisayen rundunar soji, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Juma'a.
A cewar Enenche, dakarun NAF sun kaddamar da harin ne ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, bayan samun sahihan bayanan da su ka tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun yi hijira daga bangaren dajin Kagara a jihar Sokoto zuwa wani bangare na dajin da ke jihar Zamfara.
Enenche ya kara da cewa na'urorin leken asiri na rundunar soji (ISR) sun gano daidai wurin da 'yan bindigar su ka tare a cikin dajin.
"A saboda hakane aka tura dakarun NAF da ke aiki a karkashin atisayen HADARIN DAJI zuwa wurin domin su kaddamar da hari a kan 'yan bindigar.
"A lokacin da dakarun NAF su ka tunkari wurin, sun hango tawagar 'yan bindiga da shugabanninsu a yayin da su ke neman matsuguni a cikin dajin.
"Wasu daga cikin 'yan bindigar sun yi kokarin guduwa zuwa cikin duhuwar jeji, amma hakan bai hana sojoji sakar mu su bama - bamai da alburusan bindiga ba daga sararin samaniya," a cewar jawabin.
A cewar Enenche, "daga bisani, mun gano cewa an kashe kwamandoji 8 da dumbin sauran 'yan bindiga ta hanyar amfani da fasahar bincike ta HUMINT."
A ranar Laraba ne Legit,ng ta rawaito cewa NAF ta sanar da cewa ta kashe dumbin 'yan bindiga tare da lalata sansaninsu a wani sabon hari da ta kaddamar daga sararin samaniya a kan 'yan bindiga a jihar Sokoto.
Darektan hulda da jama'a na rundunar NAF, Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata a Abuja.
Daramola ya ce babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ya sanar da cewa an kai hari sansanin 'yan bindigar ne ranar Litinin a karkashin atisayen HADARIN DAJI.
DUBA WANNAN: 'Ka fara yin murabus kafin mu hadu a kotu'- Dan jarida ya mayarwa Osinbajo martani
A cewar Abubakar, kaddamar da babban atisayen 'ACCORD' na daga cikin kokarin rundunar soji na kawo karshen ta'addancin 'yan bindiga, barayin shanu, ma su garkuwa da mutane da sauran batagari da ba sa son zaman lafiya.
Bayan ya nuna jin dadinsa da kai sabon harin, Abubakar ya ce manufar atisayen shine yi wa 'yan bindiga ruwan wuta har sai sun fito daga maboyarsu da ke dajin Kagara a jihar Sokoto.
Ya bayyana cewa dakarun NAF su na aiki bisa hadin gwuiwa tare da takwarorinsu na kasa domin tabbatar da cewa babu wasu 'yan bindiga da su ka tsira bayan an yi kuguden wuta a sansaninsu daga sararin samaniya.
A cewar Abubakar, saboda dajin Kagara ya ratsa har cikin kasar Nijar, rundunar sojin Najeriya ta na aiki tare da dakarun kasar domin tabbatar da cewa 'yan bindigar ba su sulale ta iyakar Najeriya da Nijar ba.
Babban hafsan ya ce an tura dumbin dakarun NAF zuwa Sokoto ne domin kara karfin yaki da 'yan ta'adda da rundunar soji ke yi a jihar da kewaye.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng