Majalisa ba ta ji dadin yadda Akpabio ya yi burus da zaman binciken NDDC ba

Majalisa ba ta ji dadin yadda Akpabio ya yi burus da zaman binciken NDDC ba

- A jiya aka gayyaci Godswill Akpabio gaban Majalisa, amma bai je ba

- Ministan Neja-Deltan ya bada uzurin da Sanatoci ba su gamsu da shi ba

- Daga baya Ministan ya hallarci zaman da aka yi a yau, ya wanke kansa

A ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta fito ta yi Allah-wadai da rashin halartar ministan Neja-Delta gaban majalisa a wani bincike da ake yi.

Ana binciken wasu kudi da ake zargin an wawura daga hukumar NDDC, a dalilin haka aka aikawa Godswill Akpabio gayyata zuwa majalisa a matsayinsa na Ministan harkokin Neja-Delta.

Sanata Godswill Akpabio bai samu halartar wannan zama da aka kira ba, haka zalika bai bada amsa ga takardun da ‘yan majalisar su ka rika aika masa game da batun ba.

Shugaban wannan kwamiti da ya ke binciken zargin badakala a hukumar NDDC, Sanata Olubunmi Adetunmbi ya bayyanawa ‘yan jarida wannan a jiya.

Olubunmi Adetunmbi ya koka da yadda Ministan ya yi mursisi a game da wasikun da aka aika masa domin yin bayanin binciken da ya yi a hukumar da ke kula da cigaban yankin Neja-Delta.

KU KARANTA: Jakadan Lebanon ya mike ya yi tafiyarsa yayin da zai gana da Majalisa

Majalisa ba ta ji dadin yadda Akpabio ya yi burus da zaman binciken NDDC ba
Sanata Godswill Akpabio
Asali: UGC

Ministan ta bakin sakataren din-din-din na ma’aikatar ta Neaj-Delta, Aminu Bisalla, ya bada uzurin cewa ya na wurin wasu manyan ayyuka da su ka shafi hidimar kasa.

Kwamitin da ke gudanar da wannan bincike ya nuna rashin gamsuwa da wannan uzuri na Ministan. Majalisar ta ce ba ta yi na’am da wannan a matsayin dalilin rashin zuwansa ba.

Majalisar dattawa ta na zargin cewa an batar da kusan Naira biliyan 40 a hukumar NDDC. Daga ciki, bincike ya nuna hukumar ta yi facaka da N3.1b wajen yaki da annobar COVID-19.

Labari ya zo mana yanzu nan daga jaridar The Punch cewa dazu Ministan ya amsa gayyatar sanatocin daga baya, kuma ya musanya zargin cewa ya karbi wasu kwangiloli.

Dazu Sanata Godswill Akpabio ya shaidawa tsofaffin abokan aikin na sa cewa maganar ya karbi kwangilolin Naira miliyan 500 daga NCDC ba gaskiya ba ne.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng