Jami’an ‘Yan Sanda da Ma’aikatan Hukumar Neja-Delta sun raba Biliyoyi – Majalisa

Jami’an ‘Yan Sanda da Ma’aikatan Hukumar Neja-Delta sun raba Biliyoyi – Majalisa

Majalisar dattawa da kwamitin shugabannin rikon kwarya na hukumar NNDC mai kula da cigaban Neja-Delta su na takaddama a kan zargin raba wasu Naira biliyan uku.

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar dattawan kasar ta na zargin hukumar NDDC da raba wadannan kudi Naira biliyan 3.14 ga ma’aikatanta da kuma jami’an ‘yan sanda.

Sanatoci yayin da su ke binciken wasu Naira biliyan 40 da aka wawura a NDDC, sun ce sun gano an yi bushasha da Biliyan uku da sunan tallafin yaki da annobar COVID-19.

Da aka fara sauraron ta-bakin jama’a a wannan bincike da ake yi, majalisa ta bakin shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Adetumbi ta ce an raba fiye da Biliyan uku a hukumar.

Ya ce: “Daga takardun bankin da aka aikowa wannan kwamiti daga ofishin IMC game da kudin da aka kashe tsakanin Oktoban 2019 zuwa Mayun 2020, kudin da aka batar a kan annobar COVID-19 su na da ban tsoro.”

KU KARANTA: Buhari ya sa hannu a kan sabon kasafin kudin 2020

Jami’an ‘Yan Sanda da Ma’aikatan Hukumar Neja-Delta sun raba Biliyoyi – Majalisa
Ofishin Hukumar NDDC
Asali: Facebook

Sanata Olubunmi Adetumbi ya kara da cewa:

“A cikin kason Naira biliyan 81.495 da IMC ta batar a karkashin shugabancin Gbene Nunieh zuwa Farfesa Pondei, an kashe Naira biliyan 3.14 a matsayin tallafin yaki da annobar COVID-19.”

"Wasu kudin da aka batar a kan yaki da annobar sun hada da N3m da aka ba ma’aikata 148, N1.5m da aka biya wasu rukunin ma’aikata 157, da kuma N1m ga wasu 497, sannan N600, 000 ga wasu ma’aikata 464 na dabam."

“Daga cikin kason yaki da annobar kamar yadda aka bayyana a takardun shi ne N475m da aka kashe wajen sayen takunkumin rufe fuska da ruwan wanke hannu na jami’ai a jihohi 9 da ke yankin Neja-Delta.”

Binciken ya nuna a karkashin jagorancin Daniel Pondei a shekara guda, NDDC ta kashe N59.1b. An yi amfani da biliyoyi wajen tafiye-tafiye, shari’a, ayyukan mazabu, ta’aziyya, maganin zazzabin Lassa, kudin asibiti da sauransu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng