Yakin neman zaben Edo: An fara haska bidiyon dalolin Ganduje a majigin babban shataletalen birnin Benin
- Wani bidiyon badakalar Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake bayyana
- An sanya bidiyon da ke nuna gwamnan na Kano yana zuba daloli a babbar riga a kan wani katon majigi a jihar Edo
- An dawo da bidiyon ne yayinda yan siyasa ke kokarin ganin sun kai mambobin jam’iyyar adawa kasa a bainar jama’a
Yayinda ake ci gaba da gwagwarmaya gabannin zaben jihar Edo mai zuwa, wata kungiyar mutane da ba a san ko su wanene ba sun sanya bidiyon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano yana zuba dala a aljihu a kan wani babban majigi.
Legit.ng ta tuna cewa a shekarar 2018 gwamnan Kanon ya fada a wata badakala na zargin aikata rashawa, bayan wani bidiyo da ya billo ya hasko shi yana zuba daloli a aljihu wanda aka ce cin hanci ne ya karba daga yan aikin kwangila.
An gano gwamnan yana karban daloli yana zubawa a cikin babban rigansa, wannan ya haddasa alamomin tambaya a watanni da dama da suka gabata.
Wata kafar sadarwa ta Najeriya, wacce ta fara wallafa bidiyon, ta ce kudin $230,000 da aka zargi gwamnan da karba ya kasance cikon kudade da gwamnan ya karba ne wanda gaba dayansa ya kama cin hancin dala miliyan 5.
A watan Janairu 2019, wannan jaridar ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kan ta kori karar da aka shigar na neman a binciki zargin rashawarar da ke cikin bidiyo da dama da suka bayyana.
KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Kusoshin EFCC za su amsa tambayoyi a kan binciken Magu
Gabannin zaben gwamna a jihar Edo, wanda za a gudanar a watan Satumba, sai aka sanya wannan bidiyo a katon allon majigi inda masu tafiya a kafa da mota za su iya gani.
Wani mai rajin kare hakkin dan Adam, Deji Adeyanju ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 9 ga watan Yuli.
A gefe guda, a baya mun ji cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ce jam'iyyar APC za ta yi duk yadda za ta iya don lashe zaben me gabatowa.
Ganduje ya ce Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike zai kasance a cibiyar killacewa ta jiharsa, kuma kafin ya warke za su ci zaben.
Ya ce kwamitin yakin neman zaben na cike da gogaggun 'yan siyasa da kuma matasa masu jini a jika.
Ya ce APC ta gano kokarin magudin zaben da PDP ke shirin yi kuma a shirye suke don bankade hakan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng