Yanzu Yanzu: Buhari ya sauya wasu jakadu 2 (kalli sunayensu)

Yanzu Yanzu: Buhari ya sauya wasu jakadu 2 (kalli sunayensu)

Majalisar dattawa a ranar Laraba, ta karbi wata bukata daga shugaban kasa Muhammadu Buhari na maye gurbi tare da tabbatar da wasu jakadu biyu.

Bukatar na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan ya karanto a zauren majalisar.

Shugaban kasar ya bukaci a maye nadin Mista Oboro Effiong Akpabio da na Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar wanda aka yi da farko.

Wasikar ya zo kamar haka: “daidai da sashi na 171(1)(2)(c) da karamin sashe na (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya kamar yadda aka gyara, Ina mika sunayen Mista John J. Usanga da Air Commodore Peter Anda Bakiya Gana (mai ritaya) daga jihohin Akwa Ibom da Niger domin a tabbatar da su, a matsayin jakadu.

“Ina bukatar majalisar dattawa da ta yi kiranye ga sunayen da na fara gabatarwa na Mista Oboro Effiong Akpabio da Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar daga Akwa Ibom da Borno.

“Wasikar mai kwanan wata 17 ga watan Yuni 2020, na canza sunan Mista Oboro Effiong Akpabio da na Mista John J. Usanga (jihar Akwa Ibom). Na maye gurbin Birgediya Janar Bwala Yusuf Bukar (jihar Borno) da Air Commodore Peter Anda Bakiya Gana (jihar Niger).”

Amma a karkashin sashi na 43 na tsarin Majalisar dattawa, dan majalisa mai wakiltan birnin tarayya, Sanata Philip Aduda, ya yi zanga-zanga kan ware birnin tarayya wajen nadin jakadu.

Yanzu Yanzu: Buhari ya sauya wasu jakadu 2 (kalli sunayensu)
Yanzu Yanzu: Buhari ya sauya wasu jakadu 2 Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

A cewarsa, dan birnin tarayya guda da ke jakadanci a kasar Sierra Leone, Hafiz Obada, ba a sabonta nadin nasa ba.

KU KARANTA KUMA: Tukwicin N5000 aka bani da na kashe mutane bakwai – Dan fashi

Ya bukaci a yi wani abu domin taimakawa mutanen birnin tarayya.

Ya ce: “bamu samu mukamin minista ba, bama samun abubuwa da dama, kuma dan kadan din da muka samu yana shirin kubce mana wanda bai kamata ya zama haka ba.”

A nashi bangaren shugaban majalisar dattawan, Ahmad Lawan, ya bayyana korafin dan majalisar a matsayin mai amfani, cewa kundin tsarin mulki ta ba yan birnin tarayya damar da shugaban kasa zai nada su a matsayin jakadu.

“Na taya birnin tarayya juyayi amma na san akwai jakadu 12 da aka sabonta nadinsu. Ban sani ba ko akwai dan birnin tarayya a cikin wadannan sha biyu din, amma dai korafinka na da tasiri.

“Shawarar da zan bayar shine kila ya zama dole mu dauki matakai na siyasa sosai, domin kada ya dunga zama kamar ihu bayan hari.

“Kamata ya yi a dunga daukar birnin tarayya kamar wata jiha, haka kundin tsarin mulki ya bayyana, don haka kun cancanci guda kamar kowace jiha,” in ji Lawan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel