An bindige kyaftin ɗin soja har lahira, an sace matarsa da mahaifiyarsa
Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun harbe wani jami'in sojan ƙasa da ke aiki a barikin soja ta Ojo a hanyar Okene zuwa Lokoja.
Rahotanni sun ce Kyaftin GSM Abubakar yana tafiya ne cikin motarsa ƙirar Honda Accord mai lamba N/13600 yayin da ƴan bindigan suka tare motarsa.
Wata majiya da ba a tabbatar da ingancin ta ba ta ce Abubakar ya baro Legas ne yana hanyarsa na zuwa Kwalejin Sojoji ta Jaji da ke Kaduna don halartar horon ƙananan jami'an sojoji na 2020.
DUBA WANNAN: Covid-19: Wani mutum ya siya takunkumin fuska ta gwal kan kudi N1.5m (Hotuna)
An ce yana tare da matarsa da mahaifiyarsa ne a lokacin da abin ya faru kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ƴan bindigan sun buɗe wa jami'in sojojin wuta ne inda suka kashe shi nan take duk da cewa bai saka kayan sojojin sa ba.
Daga nan kuma suka yi awon gaba da matarsa da mahaifiyarsa.
Sauran jam'ian sojojin da ke bayansa cikin motocinsu sun tsira daga harin.
An ce sun yi ƙoƙari sun zille wa ƴan bindigan sannan suka tsere daga wurin da abin ya faru.
An kai gawar jami'n sojan zuwa Cibiyar Lafiya ta Tarayya, FMC, Lokoja, inda iyalansa suka karbi gawar a ranar Talata don yi masa jana'iza a garinsu da ke jihar Niger.
A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen jihar Adamawa ta kama hatsabibin shugaban kungiyar Miyagu ta Shila, Micheal Linus.
Mr Nuradeen Abdullahi, Kwamandan Rundunar ta jihar ya gabatar wa manema labarai wanda ake zargin a ranar Talata a Yola kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Abdullahi ya ce rundunar ta hanyar tattara bayanin sirri ta kama Linus da aka fi sani da Damudu, shugaban kungiyar miyagu ta Shila da wasu miyagun biyu da rundunar ta dade tana nema.
Kwamandan ya yi bayanin cewa kafin kama shi, Linus gawurtaccen wanda ake zargi da aikata laifi ne da ya kasance yana fitinar mutanen jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng