Majalisa ta ce za ta gayyaci shugabannin NLNG da NNPC kan zargin badakala
‘Yan majalisa sun tsaida matsaya cewa za su aikawa shugaban kamfanonin mai da gas na NNPC da NLNG gayyata domin su amsa tambayoyi game da wasu zargi da ke kansu.
Majalisar wakilan tarayya ta na zargin cewa wadannan kamfanoni sun cire kudi har fam Dala biliyan 1.05 daga asusun kamfanin gas na kasa, NLNG.
Majalisar kasar ta cin ma wannan mataki ne bayan Honarabul Ndudi Elumelu mai wakiltar yankin jihar Delta a karkashin jam’iyyar PDP ya kawo shawarar a zauren majalisa a ranar Talata.
Matsayar da aka cin ma shi ne majalisar ta bukaci wani kwamitinta ya gayyaci shugabannin NNPC da kuma na NLNG domin a binciki abubuwan da su ke faruwa da asusun na Najeriya.
An ba wannan kwamiti da ke lura da dukiyar gwamnati wa’adin makonni hudu domin su gudanar da bincike, su kuma kawo rahotonsu a gaban majalisa.
Ana sa ran cewa za a kammala wannan bincike na musamman ne a cikin watan Agusta.
KU KARANTA: An fara kutun-kutun na tsige Gwamnan Imo watanni 6 da hawansa
Ndudi Elumelu ya ke cewa hukumar NNPC wanda ta ke wakiltar gwamnatin Najeriya a NLNG ta zari kudin da su ka kai Dala biliyan 1.05 daga asusun kamfanin gas din.
Idan aka yi lissafin wannan kudi da ake zargin cewa an dauka daga asusun NLNG a kudin Najeriya, za a fahimci cewa kudin ya kai kusan Naira biliyan 500.
Muddin ta tabbata NNPC ta aikata abin da ake zarginta, shakka babu ta sabawa dokar kasafin Najeriya. Ana zargin an cire kudin ne ba tare da iznin majalisa da ma’aikatun gwamnati ba.
Akwai bukatar ‘yan majalisa da ma’aikatu da manyan jami’an da ke kula da harkar kudi su san da labarin, sannan su bada shawarar duk abin da ya ke faruwa da asusun gwamnati ta ke da iko a kai.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng