Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi

Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi

- Dino Melaye ya yi ba’a ga Ibrahim Magu a kan dakatar da shi da aka yi a matsayin shugaban EFCC

- Tsohon dan majalisar dokokin ya ce ya gargadi Shugaban kasa Muhammadu Buhari game da rashin gaskiyar Magu wajen yaki da cin hanci da rashawa

- Melaye ya kuma ce akwai mutane da yawa a majalisar shugaban kasar da ke satar dukiyoyin kasa kamar irin na shugaban na EFCC

Dino Melaye, tsohon dan majalisa mai wakiltan Kogi ta yamma, ya yi ba’a ga Ibrahim Magu, shugaban hukumar EFCC biyo bayan dakatar da shi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Shugaban kasar ya shata wa Magu layi a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, ta hanyar dakatar da shi sa’o’i 24 bayan hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyace shi da kuma tsare shi.

Bata tsayawa Shugaban na EFCC a nan ba kawai domin wata tawagar hadin gwiwa na jami’an yan sanda da DSS sun je gidansa da ke babbar birnin tarayya Abuja, sannan suka bincike koina.

An tattaro cewa jami’an tsaro sun mamaye gidan Magu na kansa da ke a Karu, wani yanki da ke Abuja da kuma gidansa na gwamnati da ke Maitama.

Da yake martani ga lamarin Magu, tsohon dan majalisar ya je shafinsa na Twitter domin yi wa shugaban hukumar yaki da rashawar ba’a.

Ya ce ya yi gargadi a kan Magu amma Shugaba Buhari bai sauraresa ba.

KU KARANTA KUMA: Daukan ma’aikata 774,000: Keyamo ya sake caccakar majalisa duk da hakurin da babban minista ya bayar

Melaye, wanda ya wallafa wani bidiyonsa yana waka, ya ce yanzu shugaban kasar ya ga shaidanin da ke tattare da yaki da rashawar Magu.

Ya ce akwai mutane da dama a gwamnatin Buhari wadanda ke satar baitul malin kasar yayinda suke nuna su tsarkakku ne a bainar jama’a.

Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi
Ibrahim Magu: Dino Melaye ya yi martani a kan dakatar da shugaban EFCC da Buhari ya yi Hoto: The Punch
Asali: UGC

A halin da ake ciki, mun ji a baya cewa Magu, ya fitar da wasu daga cikin kayayyakinsa da ke hedkwatar hukumar, jaridar Tribune Online ta ruwaito.

A cewar wasu majiyoyi na tsaro, shugaban na EFCC ya umurci hadimansa da su fitar da kayayyakinsa daga ofis din a safiyar ranar Talata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel