RAP ta nemi Alkali ya bayyana Emeka Ihedioha a matsayin Gwamnan Imo
- Akwai yunkuri da ake yi na sauke Hope Uzodinma daga kujerar Gwamnan Imo
- Kujerar Uzodinma ta na rawa bayan kotu ta ce Uche Nwosu ne ainihin ‘dan takarar APC
Gwamnan jihar Imo Sanata Hope Uzodinma ya na fuskantar kalubale a kan mulki a dalilin wata shari’a da aka fara yi a kotun babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar The Sun ta ce jam’iyyar RAP da ‘dan takararta a zaben jihar Imo, Okere Kingdom sun kai kara a kotu, su na neman Alkali ya fede masu matsayar takarar Hope Uzodinma a APC.
Okere Kingdom su na kalubalantar takarar Hope Uzodinma a jam’iyyar APC. Jam’iyyar hamayyar ta na nuna tantama a kan cewa APC ta ba gwamnan mai-ci tuta a zaben 2019.
Masu karar a kotu su na bukatar Alkali ya tursasawa hukumar zabe na kasa watau INEC ta karbe takardar nasarar da ta ba gwamna Hope Uzodinma.
KU KARANTA: Shugabannin APC sun bayyana yadda ta kaya bayan an yi zama da su Tinubu
Lauyoyin jam’iyyar hamayyar da kuma ‘dan takararta, su na so kotu ta ba ‘dan takarar jam’iyya PDP kuma tsohon gwamnan jihar watau Emeka Ihedioha, nasara a zaben 2019.
Masu kare jam’iyyar RAP sun dogara ne da hukuncin da kotun koli ta yi a shari’a mai lamba ta SC/1384/2019 inda ta ce babu shakka Ugwumba Uche Nwosu ne ‘dan takarar APC a zaben Imo.
A farkon shekarar nan ne kotun koli ta ba mutane da-dama mamaki, ta bayyana Hope Uzodinma a matsayin zababben gwamnan jihar Imo duk da ya na bayan Ugwumba Uche Nwosu da Emeka Ihedioha.
Kotun koli ta yi wannan shari’a ne bayan Emeka Ihedioha ya lashe zaben gwamnan Imo, ya kuma yi nasara a kotun sauraron karar zabe, ya kuma shafe watanni kusan bakwai a kan mulki.
A majalisar jihar Imo kuma, ‘dan majalisar yankin Oguta, Frank Ugboma, ya musanya rade-radin da ke yawo na cewa su na shirin tsige Hope Uzodinma.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng