Darektan gudanarwa, Mohammed Omar zai jagoranci EFCC na rikon kwarya

Darektan gudanarwa, Mohammed Omar zai jagoranci EFCC na rikon kwarya

- Ana rade-radin cewa hukumar EFCC ta nada sabon Shugaba na rikon-kwarya

- Mohammed Omar zai haye kujerar EFCC yayin da ake binciken Ibrahim Magu

- Hukumar ba ta iya tabbatar da wannan canji da aka samu a cikin makon nan ba

A daidai lokacin da Ibrahim Magu ya ke cigaba da zama a hannun jami’an tsaro inda ake bincikensa da zargin laifuffuka a EFCC, hukumar ta nada sabon shugaban riko.

Kwana biyu kenan a jere Ibrahim Magu ya shafe ya na amsa tambayoyi daga wani kwamiti na musamman da shugaban kasa ya kafa a karkashin jagorancin Ayo Isa Salami.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa jaridar Vanguard cewa an taso Magu a gaba ne domin ya wanke kansa daga zargin da ake yi masa na yin ba daidai ba a hukumar EFCC.

Majiyar ta ke cewa: “Babu wanda ya fi karfin a tuhume shi a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari. Babu wanda ya fi karfin haka.”

A halin da ake ciki kuma, hukumar ta nada Mista Mohammed Umar a matsayin wanda zai jagoranci harkokin EFCC har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake yi.

KU KARANTA: Shugaban Najeriya ya dakatar da Shugaban yaki da barayi

Darektan gudanarwa, Mohammed Omar zai jagoranci EFCC na rikon kwarya
Ibrahim Magu
Asali: Depositphotos

Wani babban jami’in EFCC ya shaidawa hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN cewa an zabi Mohammed Umar ya zama shugaban riko a dalilin dakatar da Ibrahim Magu.

Rahoton ya bayyana cewa hukumar ta duba matsayi ne kafin ta dauki wannan mataki. Umar shi ne darekta na harkokin gudanarwa a hukumar EFCC, kuma babban jami’i ne.

Sai dai mai magana da yawun bakin hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa, Dele Oyewale, bai iya tabbatar da wannan cigaba da aka samu ba.

Da aka tuntubi Kakakin hukumar watau Mista Dele Oyewale, ya gagara yi wa ‘yan jarida bayani.

A game da dakatarwar da aka yi wa Ibrahim Magu, EFCC ta fito ta kare shugabanta daga zargi, ta ce bai aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su ba, a cewarsu sharar fagen siyasar 2023 ake yi.

Amma kuma wasu ma’aikatan EFCC su na kuka da Magu inda su ke zargin cewa ana yi masu kauron kudi, tare da hana su samun karin matsayi a wurin aiki.

Magu wanda ya kasance mukaddashin shugaba a EFCC tun 2015 ya na gamuwa da barazana iri-iri a yanzu. A ranar Talata ne ‘yan sanda su ka shiga gidansa, su ka yi wani lalube.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel