Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000

Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000

Ministan kwadago, Chris Ngige, a ranar Talata, ya ba majalisar dokokin tarayya hakuri a kan musayar yawun da ya barke tsakaninsu da karamin ministan kwadago.

Idan za ku tuna an dai yi musayar yawu tsakanin Festus Keyamo da kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokokin kan ayyukan ma’aikatar.

Keyamo ya samu sabani da kwamitin majalisar kan tsarin aiwatar da shirin diban ma’aikata na musamman wanda gwamnatin tarayya za ta dauki matasa 774,000 a kasar.

Ana sanya ran biyan wadanda suka amfana da shirin N20,000 duk wata daga watan Oktoba zuwa Disamba 2020.

Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000
Yanzu Yanzu: Ngige ya bayar da hakuri a kan furucin Keyamo game da ayyuka 774,000 Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ngige ya bayar da hakurin ne a lokacin da ya kai ziyarar amsa gayyatar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi masa a Abuja.

Keyamo da sauran manyan jami’an ma’aikatar na cikin tawagar da suka yi wa ministan rakiya.

Ngige ya bayyana cewa matsayar Keyamo a wasikarsa da ke ta yawo a ranar Litinin bai kasance mai muhimmanci ba.

Lawan ya ce lallai dukkanin matakan da Keyamo ya riga ya dauka kan shirin sun kasance marasa inganci.

Ya kara da cewar hukumar daukar ma’aikata ta kasa (NDE) ce ya kamata ta aiwatar da shirin.

Sannan ya kuma sha alwashin cewa majalisar dokokin tarayya za ta dakile duk wani yunkuri da ma’aikatar za ta yi don kwace shirin.

A baya Festus Keyamo ya fallasa cewa cikin ma’aikata 774,000 da gwamnatin tarayya zata dauka majalisar kadai ta zaftare kashi 15% , wanda yayi daidai da akalla mutum 116,100.

Keyamo ya bayyana haka da yake halartar taron kwamitin majalisar domin tattauna yadda za a raba ayyukan da kuma inda aka kwana.

KU KARANTA KUMA: Magu: Babu wanda ya fi karfin bincike – Fadar shugaban kasa

Hakan ya haddasa rudani domin dai ana cikin taron a ka barke da jefa wa juna zafafan kalamai.

Idan za ku tuna, Shugaba Muhammadu Buhari yayi alƙawarin fidda ‘yan Najeriya sama da miliyan 100 daga kangin talauci a dan kankanin lokaci.

Hakan yasa ake ta kirkiro shirye-shirye da zai samar da haka a kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel