Hushpuppi: APC ta fitar da bidiyo da ke nuna tarayyar Hushpuppi da ‘Yan PDP

Hushpuppi: APC ta fitar da bidiyo da ke nuna tarayyar Hushpuppi da ‘Yan PDP

Jam’iyyar APC ta hakikance a kan cewa wasu daga cikin ‘ya ‘yan PDP su na da alaka da Ramon Igbalode Abbas, wanda ake zargi da laifin damfar da zamba cikin aminci.

APC mai mulki a wani jawabi da ta fitar a ranar 4 ga watan Yuli, 2020. ta bakin tsohon kakakinta, Yekini Nabena, ta ce gawurtaccen ‘dan damfarar ya na tare da wasu ‘yan jam’iyyar adawa.

Mista Yekini Nabena ya yi kira ga hukuma ta binciki abin da ke tsakanin manyan jam’iyyar APC da wannan mutumi da aka fi sani da Ray Hushpuppi.

Yanzu haka Igbalode Abbas ‘Hushpuppi’ ya na hannun jami’ai a kasar Amurka bayan an tattara keyarsa daga birnin Dubai a kasar UAE da zargin cewa ya damfari miliyoyin mutane.

Jagororin PDP sun karyata wannan zargi da ya fito daga bakin abokan gaban na su, sun ce kanzon kurege ne kurum na jam’iyyar mai mulki.

KU KARANTA: Ba mu cafke Magu ba - DSS

Hushpuppi: APC ta fitar da bidiyo da ke nuna tarayyar Hushpuppi da ‘Yan PDP
Hushpuppi da wasu jagororin PDP
Asali: UGC

Yayin da ake cikin wannan dambarwa, jam’iyyar APC ta reshen kasar Birtaniya ta fito da bidiyon da ke nuna Huspuppi da irinsu Dino Melaye da Timi Frank.

APC ta fito da wannan bidiyo ne a shafinta na Twitter inda aka ga tsohon Sanatan na Kogi da tsohon kakakin jam’iyyar APC - wanda yanzu ya koma PDP su na wasa da dariya tare da Huspuppi.

Daya daga cikin wanda aka jefa da zargin kusanci da Huspuppi shi ne Yakubu Dogara. Tsohon shugaban majalisar wakilan Najeriyar ya karyata wannan zargi.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya ce a shirye ya ke ya tafi kurkuku idan aka yi bajakolin hujjojin da ke nuna akwai wata dangantaka tsakaninsa da Huspuppi.

APC ta ce wannan bidiyo da ta fitar shi ne wanda jagororin jam’iyyar PDP ba su so jama’a su gani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel