Edo 2020: Za mu killace Wike, kafin ya dawo mun lashe zabe - Ganduje
Shugaban kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar Edo karkashin jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya ce jam'iyyar za ta yi duk yadda za ta iya don lashe zaben me gabatowa.
Ganduje ya ce Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike zai kasance a cibiyar killacewa ta jiharsa, kuma kafin ya warke za su ci zaben.
Ya ce kwamitin yakin neman zaben na cike da gogaggun 'yan siyasa da kuma matasa masu jini a jika. Ya ce APC ta gano kokarin magudin zaben da PDP ke shirin yi kuma a shirye suke don bankade hakan.
Jam'iyyar PDP ta bayyana Gwamna Wike a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabenta na jihar Edo.
Amma yayin jawabi a ranar Litinin bayan kaddamar da kwamitin yakin neman zaben, Gwamna Ganduje ya ce PDP tana goyon bayan Gwamna Godwin Obaseki ne saboda suna son dibar tarin dukiyar da jihar ta tara don zaben.
Ganduje ya zargi Obaseki da butulci. Ya ce APC ce tsatsonsa amma duk da haka ya juya mata baya.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: DSS ta hana 'yan jarida shiga inda ake tuhumar Magu a Aso Villa
Ya ce, "Da farko dai, gani ya kori ji. Tun daga ganin kwamitin yakin neman zaben, kun san APC ta shirya wa zaben kuma za ta yi duk abinda ya dace wajen tabbatar da ta yi nasara a zaben.
"Abinda yasa nake fadin haka shine, a kwamitin nan an hada da tsoffin 'yan siyasa da kuma matasa masu jini a jika wadanda yanzu suke tasowa.
"Dukkanmu muna da saiti kuma bamu faduwa. A don haka ne muke tabbatar wa kanmu cewa a shirye muke don aikin nan.
"Amfanin wannan kwamitin shine samar da muhalli ga dukkan 'yan jam'iyyar da wadanda ba 'ya'yanta ba domin samun yin zabe cike da lumana da kwanciyar hankali."
Ya kara da cewa, "mun san jam'iyyar adawa na kokarin yin magudi kuma mun san salonsu da inda suka kware. Za mu bankade dukkan salon nan wurin ganin mun yi nasara.
"Mun san PDP ta saka Wike kan gaba, amma muna tabbatar muku da cewa zamu killace shi a cibiyar killacewa kuma kafin ya warke, mun kammala zaben.
"PDP ta yanke shawarar bai wa tsohon gwamnan mu wurin zama ne saboda sun ga yana rike da dukiyar jihar Edo kuma suna son yin amfani da ita don zaben.
"Amma ina tabbatar muku da cewa mutanen jihar Edo na kallon komai. Sun san wanda aka taimaka a zaben 2016 ya mika baitul malinsu ga PDP don ya ci zabe. Jama'ar jihar ba za su amince da butulci ba. Za su fito a ranar 19 ga wata don zaben jam'iyyar APC."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng