Shin Zulum ya ce ba zai yi wa APC kamfen ba a Edo?
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya nesanta kansa daga wani labari da aka wallafa kuma ya ke yawo a kafofin sadarwa, wanda aka alakanta da shi kan zaben gwamnan jihar Edo.
Zulum ya bayyana wannan labari da aka wallafa a matsayin 'kanzon kurege' da makircin magauta.
A cikin labarin da aka wallafa, an yi ikirarin cewa Gwamna Zulum ya ce ba zai zubar da martabarsa ba a idanun duniya ta hanyar zuwa jihar Edo domin jagorantar kamfen din jam’iyyar APC bayan ganin dukkanin abubuwan da Oshiomhole ya fadi a kan dan takararta a 2016.
An bayyana cewa Zulum ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta cewa; “ba zan taba zubar da kimata ba ta hanyar zuwa jihar Edo domin jagorantar kamfen din jam’iyyar APC bayan ganin dukkanin abubuwan da Oshiomhole ya fadi game da dan takararta a 2016 – Gwamna Zulum.”
Sai dai, a cikin wani sako da ya fitar a ranar Litinin, gwamnan ya karyata wannan batu da aka jingina da shi a shafinsa na Twitter inda ya ce shi cikakken dan APC ne kuma yana goyon bayan duk wani dan takara da jam’iyyar ta tsayar a fadin kasar.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su yi watsi da wannan batu da aka jingina da shi.
KU KARANTA KUMA: Cutar korona: Sakamakon gwajin iyalan Gwamna Lalong ya fito
Zulum ya wallafa a shafinsa na twitter ta @ProfZulum cewa: “Labarin karya!
“Dan Allah ku yi watsi da wannan makircin. Bai fito daga gareni ba kuma ba zai taba fitowa daga gareni ba. Ni cikakken dan APC ne kuma ina goyon bayan dukkanin yan takarar jam’iyyar @OfficialAPCNg dari bisa dari a kowani yanki na Najeriya.”
A wani labarin kuma, Aliko Dangote, hamshakin mai kudin Afrika ya musanta batun goyon bayan Godwin Obaseki, gwamnan jihar Edo a karo na biyu da yake neman zarcewa.
Da yake magana ta hannun mai magana da yawunsa, Anthony Chiejina, Dangote ya bayyana rahoton cewa yana goyon bayan Obaseki a matsayin wani yunkuri na bata masa suna, jaridar The Cable ta ruwaito.
Ya ce a matsayinsa na shugaba a fagen kasuwanci, ya mayar da hankali wajen ci gaba, samar da ayyukan yi da kuma taimakon jama'a ba wai siyasa ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng