Cutar korona: Sakamakon gwajin iyalan Gwamna Lalong ya fito

Cutar korona: Sakamakon gwajin iyalan Gwamna Lalong ya fito

- Sakamakon gwajin cutar korona da aka yi wa Simon Lalong, iyalansa da sauran hadimansa ya nuna basa dauke da ita

- Gwamna Lalong da ahalinsa sun yi gwajin cutar korona bayan kamuwar kwamishinansa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnan.

- Lalong ya jaddada cewa kamuwa da cutar ba busharar mutuwa bace, ya shawarci jama'ar jihar da su kiyaye lafiyarsu

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, iyalansa da sauran hadimansa duk sakamakon gwajin koronar da aka yi masu ya nuna basu dauke da cutar.

Daraktan yada labarai na gwamnan, Makut Macham, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Lahadi.

Ya yi bayanin cewa Gwamna Lalong da ahalinsa sun yi gwajin cutar korona bayan kamuwar kwamishinansa da shugaban ma'aikatan fadar gwamnan.

Macham ya ce gwamnan da iyalansa sun sake yin gwajin a ranar Asabar, bayan gwajin da suka yi a farkon watan Afirilu wanda ya nuna basu dauke da cutar.

A martaninsa, Gwamna Lalong ya ce, "Ina ci gaba da shawartar mutane da su kai kansu wajen gwajin cutar korona don hakan na da amfani. Hakan zai kawo dakilewar yaduwar cutar.

Cutar korona: Sakamakon gwajin iyalan Gwamna Lalong ya fito
Cutar korona: Sakamakon gwajin iyalan Gwamna Lalong ya fito Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

"Mika kaina da iyalaina don wani gwaji na daga cikin misali na shugabanci nagari da kuma daukar mataki bayan kamuwar kwamishinonina da shugaban ma'aikatana."

Gwamnan ya jaddada cewa kamuwa da cutar ba busharar mutuwa bace, ya shawarci jama'ar jihar da su kiyaye lafiyarsu.

KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban APC na arewa maso yamma, Inuwa Abdulkadir, ya rasu

Kamar yadda yace, za a samu hakan ne bayan kiyaye dokokin yaki da cutar na amfani da takunkumin fuska, nesa-nesa da juna, wanke hannu da amfani da sinadarin tsarkake hannu.

Gwamna Lalong ya bayyana cewa a halin yanzu, jihar ta kara yawan wadanda take gwadawa na cutar a fadin jihar.

Ya kara da cewa ana kokarin kara yawan wadanda ake wa gwajin cutar a jihar. An gwada mutum 6,000 a fadin jihar a halin yanzu.

A baya mun kawo maku cewa Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya umurci mambobin majalisar zartarwa ta jihar da su je su yi gwajin cutar korona bayan wani kwamishina ya kamu da cutar.

Ya bayyana cewa bayan sun gabatar da kansu domin gwaji su yi gaggawan killace kansu daga ranar Laraba.

Umurnin Lalong na zuwa ne bayan kwamishinan kasuwanci da masana’antu, Abe Aku ya kamu da cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel