Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun nutse a hatsarin jirgin ruwan Benue

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun nutse a hatsarin jirgin ruwan Benue

- Hatsarin jirgin ruwa ya cika da wasu mutane masu yawa a kogin Benue

- An tattaro cewa jirgin ruwan na dauke da fasinjoji 28 a cikinsa

- Zuwa yanzu dai gawar mutum daya kacal aka gano

Labari da ke zuwa mana ya nuna cewa mutane da dama sun nutse a cikin kogin Benue biyo bayan wani hatsari na jirgin ruwa.

An tattaro cewa jirgin ruwan na dauke da fasinjoji 28 a cikinsa.

Mafi akasarin fasinjojin da ke cikin jirgin da ya kife sun kasance ‘yan coci da za su babban taron shekara.

Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun nutse a hatsarin jirgin ruwan Benue
Yanzu Yanzu: Mutane da dama sun nutse a hatsarin jirgin ruwan Benue Hoto: The Cable
Asali: UGC

Jaridar The Nation ta tattaro cewa gawar mutum daya aka gano a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

An gano masu shiga ruwa wadanda mafi akasarinsu masu kamun kifi ne, sun shiga suna ta kokarin nemo mutanen da abun ya cika da su.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Hawaye sun kwaranya yayinda manyan yan Najeriya 3 suka mutu sakamakon cutar a rana 1

Lamarin ya afku ne a hanyar Kwaghter a yankin Innongu na jihar Benue.

A wani labari na daban, Majalisar dinkin duniya ta kushe harin da aka kai wa daya daga cikin jiragenta a yankin Damasak da ke Borno.

Mummunan al'amarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Yuli wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu da ya hada da yaro mai shekaru biyar.

A don haka, majalisar dinkin duniya ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta bincike tare da daukar mataki a kam hakan.

A wata takarda da majalisar ya fitar a ranar Asabar kuma shugaban kula da walwala tare da jin dadi na majalisar a Najeriya, Edward Kallon, yasa hannu, ya ce harsasan da mayakan suka sakarwa jirgin saman ne ya kabo shi tare da illa ga ayyukansu a yankin.

Kallon ya ce, “Ina bakin cikin sanar da cewar an harba wa jirgin agaji na majalisar dinkin duniya harsasai a lokacin harin. Babu ma'aikacin taimako da ke jirgin kuma matukan duk sun sauka lafiya.

"Tunanina na tare da matukan kuma na jinjina musu da yadda suka sauka duk da halin da jirgin yake ciki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng