Tsige shugaban APC: Jama’a sun dasa ayar tambaya a kan rashin jin doriyar matar Oshiomhole

Tsige shugaban APC: Jama’a sun dasa ayar tambaya a kan rashin jin doriyar matar Oshiomhole

- An daina jin doriyar uwargidar tsohon shugaban jam'iyyar APC, Lara Oshiomhole a kafofin sada zumuntar zamani na tsawon lokaci

- Rashin ganinta a cikin jama'a tare da mijinta ya sa jama'a sun da ayar tambayoyin

- A 2016 ne dai aka yi ta rade-radin cewa sun rabu da Oshiomhole, sai dai kakakin tsohon gwamnan ya karyata hakan

Matar tsohon gwamnan jihar Edo kuma tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, Lara, an daina jin ta a kafofin sada zumuntar zamani na tsawon lokaci.

Amma kuma wannan shirun yasa ake ta tambayoyi a kan ta tare da fatan ko tana lafiya.

Rashin ganinta a cikin jama'a tare da mijinta ya kara tsananta wadannan tambayoyin, jaridar The Punch ta ruwaito.

Da aka duba shafukanta na kafafen sada zumuntar zamani da suka hada da Facebook, Twitter da Instagram, sun nuna cewa Lara wacce ta kasance 'yar asalin Cape Verde ta dade bata hau ba kuma rabon da tayi wata wallafa tun 2017.

Tsige shugaban APC: Jama’a sun dasa ayar tambaya a kan rashin jin doriyar matar Oshiomhole
Tsige shugaban APC: Jama’a sun dasa ayar tambaya a kan rashin jin doriyar matar Oshiomhole Hoto: Daily Post
Asali: UGC

A 2016, an bayyana cewa sun rabu da Oshiomhole, lamarin da yasa mai magana da yawun Oshiomhole, John Mayaki, ya fito ya musanta hakan. Ya tabbatar da cewa tana nan tana morar aurenta.

KU KARANTA KUMA: APC na yin kazamar siya - Saraki da Atiku sun musanta alaka da Hushpuppi

Amma kuma, saboda rikicin siyasar da mijinta ya shiga a cikin kwanakin nan, mutane da yawa sun dinga tsammanin jin ta bakin matar ko za ta nuna goyon bayan ta ga mijinta. Sai dai kash! Har yanzu bata fito tayi wani bayani ba ko aka ganta.

A wata tattaunawar da aka taba yi da Lara, ta kwatanta Oshiomhole da mutumin kirki kuma mai nuna kaunarsa ga 'ya'yansa wanda baya kai wani rikicin siyasa cikin gida.

A wani labarin kuma, PDP ta ce ta bankado makircin da jam'iyyar APC ke son shiryawa a zaben kujerar gwamnan jihar Edo ta hanyar amfani da gwamnoninta guda uku; Dakta Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, Hope Uzodinma na jihar Imo da Yahaya Bello na jihar Kogi.

Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta tsayar da ranar 19 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a kada kuri'a a zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng