Tauraron ‘Dan wasa Messi na iya barin Barcelona a karshen kakar shekarar baɗi

Tauraron ‘Dan wasa Messi na iya barin Barcelona a karshen kakar shekarar baɗi

Akwai kishin-kishin da ake ji cewa shugabannin kungiyar Barcelona su na samun matsala da babban ‘dan wasan gaban kulob din watau Lionel Messi.

Rahotannin da ke fitowa daga kasar Sifen su na nuna cewa Lionel Messi ya fara yi wa Barcelona barazanar tashi daga kungiyar da zarar wa’adinsa da ya ke ci ya zo karshe a badi.

Lionel Messi ya na tunanin barin Barcelona a karshen kakar 2021 ne a sakamakon matsaloli da-dama da ake samu tsakaninsu kamar yadda jaridun kasashen waje su ka bayyana.

Gidan rediyon Cadena Ser na kasar Turan ya ce ‘dan kwallon na Argentina ya yi watsi da maganar sabunta kwantiragin da ya rattaba hannu a kai a shekarar 2017.

‘Dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa da mahaifinsa, Jorge Messi sun shiga maganar sabuwar kwangila da kungiyar Barcelona, amma tun tuni an gaza yin gaba, an gaza yin baya.

Har yanzu da mu ke magana Lionel Messi ya ki yin na’am da sabon kwantiragi, wanda hakan ya sa jaridar The Sun ta ke ganin cewa gwarzon ‘dan wasan na Duniya ya na shirin tashi.

KU KARANTA: Messi ya yi fada da Antoine Griezmann a Barcelona

Tauraron ‘Dan wasa Messi na iya barin Barcelona a karshen kakar shekarar baɗi
'Dan wasa Lionel Messi
Asali: UGC

Rikicin Messi da manyan Barcelona ya cabe ne tun bayan da aka fara zargin ‘dan wasan gaban da hannu wajen korar koci Ernesto Valverde mai shekaru 56.

Akwai jita-jitar cewa ‘dan kwallon ya kuma fara samun matsala da sabon koci Quique Satien kafin a je ko ina, tuni shi ma an fara jin kishin-kishin din ana neman korar shi daga aiki.

Yanzu haka manyan abokan gaba watau kungiyar Real Madrid sun dare kan teburin gasar La-liga bayan rashin nasarar da Barcelona ta samu a hannun Atheltico Madrid a cikin makon nan.

Messi ya zo Barcelona ne tun ya na da shekara shida a Duniya. A tsawon shekarun da ya yi a kungiyar ya ci kwallaye 630, ya kuma lashe kofi da kyaututtuka rututu a zamansa.

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya yi magana game da rade-radin, ya ce ba zai so ganin ‘dan wasan ya bar Sifen ba. Zidane ya bayyana haka ne a ranar Alhamis bayan wasan Getafe.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel