A fito da Kwafral Martins da Mai dakinsa Victoria ldakpein - Majalisar Wakilai
Majalisar wakilan tarayya a zaman da ta yi ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli, 2020, ta bukaci kwamitin da ke lura da harkar gidan soja ya sa baki a sa-in-sar da ake yi da wani jami’i.
Jaridar This Day ta ce wannan kwamiti zai zauna da shugabannin sojoji domin ganin ayi maza an saki Lans Kwafral Martins ldakpein da matarsa Victoria ldakpein, wadanda ke tsare.
A cikin watan Yuni, Lans Kwafral Martins ldakpein ya fito a wani bidiyo ya na sukar hafsun sojojin kasar nan da cewa ba su yin abin da ya kamata wajen kawo karshen kashe-kashen da ake yi.
Honarabul Ndudi Elumelu shi ne ya gabatar da wani kudiri mai taken: “Kira ga sojojin Najeriya su saki Lans Kwafral Martins ldakpein da ke tsare saboda ya bayyana ra’ayinsa.” a majalisa.
A maimakon su gyara aikinsu, Ndudi Elumelu ya zargi manyan sojojin kasar da kuma wannan karamin soja da ya soke su a bidiyo. Elumelu ya ce hakan ya sabawa dokar Najeriya.
KU KARANTA: Aisha Buhari da Matan Gwamnoni sun ziyarci iyalin Marigayi Ajimobi
‘Dan majalisar ya ce an dauke sojan daga Sokoto zuwa garin Abuja saboda ya soki hafsun kasar. A cewar Elumelu, cafke sojoji saboda sun koka, ya sabawa doka da kudin tsarin mulkin kasar.
“Duk da sashe na 121 na dokokin gidan soja ya ba sojoji damar cafke jami’in tsaro, amma sashe na 122(6) na dokar ya nemi a fito da wanda aka tsare muddin yin hakan ba zai kawo matsalar tsaro ba.”
“Babu inda Martins ldakpein ya zama barazana ga tsaron kasa. Amma har yau ya na tsare da mai dakinsa wanda aka cafke saboda ta nemi a fito da shi.” Inji Ndudi Elumelu a jiya/
Majalisar ta bukaci kwamitin na ta ya binciki zargin da ake yi na cewa an tsare wannan soja da mai dakinsa. Bayan haka za a gayyaci sojan ya bayyana a gaban zauren kwamitin majalisar.
An cin ma matsayar cewa ldakpein zai bayyana a gaban kwamitoci da shugabannin majalisa domin ya yi masu bayanin duk abin da ya sani game da yakin da ake yi a Arewa maso gabas.
Watakila idan Martins ldakpein ya fito, ya zo gaban majalisa, ya fasa-kwai a rikicin Boko Haram.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng