Kungiyoyi da ‘Yan siyasa sun fara fafutukar ganin Ibo sun karbi mulkin kasa

Kungiyoyi da ‘Yan siyasa sun fara fafutukar ganin Ibo sun karbi mulkin kasa

Kungiyar kabilar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo, da irinsu Alaigbo Foundation, Igbo National Congress, da wasunsu, su na ganin zai yiwu Ibo ya karbin Najeriya a 2023.

A ranar Laraba ne wadannan kungiyoyi su ka fito su na cewa za su iya cin ma wannan buri na su.

Hakan na zuwa ne bayan tsohon sojan Biyafara kuma Basarake a kasar Enugu, Igwe Spencer Ugwuok, ya ce zai yi wa Ibo wahala su hau kujerar shugaban Najeriya a wannan marra.

Mai martaba Igwe Spencer Ugwuok ya zargi mutanensa da cewa: “Ndigbo ba su da hadin-kai.” Sarkin na Obimo a yankin Nsukka ya na ganin Ibo ba za su iya hada-kai su nemi mulki ba.

Ganin cewa babu jagoranci a yankin Inyamurai, Sarkin ya ce: “Mun ga mu’ujizozi iri-iri a kasar nan, amma ina fada maku cewa babu abin da ke nuna cewa Ibo zai zama shugaban Najeriya a 2023.”

Sarkin ya ce ko da ya ke shugaban kungiyar Ohanaeze Ndigbo a Duniya, Cif Nniah Nwodo, ya karawa kabilar daukaka, duk da haka Igwe Ugwuok ya na ganin akwai 'yan zagon-kasa.

KU KARANTA: Shugabannin APC na riko sun gana da Tinubu domin ayi sulhu

Kungiyoyi da ‘Yan siyasa sun fara fafutukar ganin Ibo sun karbi mulkin kasa
Jagoran kungiyar Ohanaeze Ndigbo
Asali: UGC

“Dole mu koma ga Ohanaeze Ndigbo, mu tabbatar kungiyar ce ta ke magana da yawun bakin duk wani Ibo. A yanzu ba mu da jagoranci, wanda hakan ya sa ba mu iya magana da yawu daya.”

“Sai ka ji ana cewa Ohanaeze Ndigbo ta reshen Legas, Abuja, Jos, Afrika ta Kudu da sauransu. Wannan ba daidai ba ne, shi ya ke jawo mana matsala a siyasa.” Inji Igwe Spencer Ugwuok.

Basaraken ya ce a sauran wurare Talakawa ba su fitowa su yi wa Oba na kasar Benin da Sultan watau Sarkin Musulmi raddi idan sun yi magana, akasin abin da Ibo su ke yi wa juna.

Ya ce “Ba zai yiwu ku yi wa gwamnatin Buhari adawa ba, sai kuma ya dauki mulki ya ba ku a 2023.” Amma wasu 'yan siyasa da kungiyoyin yankin su na ganin ba haka abin ya ke ba.

Uche Achi-Ogbaga ya yi wuf ya maidawa Igwe Ugwuoke a madadin kungiyar Ohanaeze Ndigbo. Ya ce Ibo su na aiki a kasa na ganin sun cin ma wannan manufa a zabe mai zuwa.

Wannan shi ne ra’ayin tsohon Ministan Najeriya Cif Mbazulike Amechi. Dattijon ya yi kaca-kaca da masu cewa Ibo za su yi mulki ba, ya ce a hakar siyasa, babu abin da ba ya yiwuwa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng