Kotu ta hana belin Wadume, ta garkame shi a gidan yari

Kotu ta hana belin Wadume, ta garkame shi a gidan yari

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bada umarnin ci gaba da tsare Hamisu Bala Wadume, wanda ake zargi da garkuwa da mutane.

Mai shari'a Binta Nyako ta bada wannan umarnin bayan bukatar belin da Wadume da wasu mutum shida da ake kara suka nema.

Nyako ta bada umarnin tsare dukkan wadanda ake kara daga sashen yakar fashi da makami zuwa gidan gyaran hali da ke Kuje.

Ta kara bai wa shugaban gidajen gyaran hali na Najeriya umarnin tabbatar da cewa sun samu kular masana kiwon lafiya da kuma bai wa lauyoyinsu damar ganinsu.

Nyako, wacce ta ce za ta gaggauta yin shari'ar, ta kara da cewa bata ga dalilin da zai sa ta bada belinsu ba.

Kotu ta hana belin Wadume, ta garkame shi a gidan yari
Kotu ta hana belin Wadume, ta garkame shi a gidan yari Hoto: The Cable
Asali: UGC

An gurfanar da Wadume ne tare da Aliyu Dadje, sifetan dan sanda, Auwalu Bala wanda aka fi sani da omo razor, Uba Bala, wanda aka fi sani da Uba Delu, Bashir Waziri, wanda aka fi sani da Baba runs, Zubairu Abdullahi wanda aka fi sani da Basho da kuma Rayyanu Abdul.

An gurfanar da su karkashin ofishin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya a kan laifuka 12 da ake zargin su da shi.

Yunkurin kama Wadume ya kai ga kisan jami'an 'yan sanda uku da wani farar hula daya a jihar Taraba a ranar 16 ga watan Augusta 2019.

A halin da ake ciki, an kira shaida biyu a ranar Laraba domin su bayar da shaida.

Hafizu Bala, shaida na biyu daga masu gurfanarwa, ya gabatar da kansa a matsayin mai sana'ar walda. Ya ce Tijjani Balarabe, sojan Najeriya mai mukamin kyaftin ya dauke shi aikin balle makulli.

Ya ce bayan isarsa, ya gano cewa Balarabe ya yaudaresa ne don ya balle ankwar da ke hannun Wadume.

KU KARANTA KUMA: Sunaye: Buhari ya rantsar da shugaba, mambobin hukumomin FCC da RMAFC

"Ina zaune a shagona yayin da Balarabe ya zo ya daukeni don balle masa kwado," yace.

"Mun isa sansanin sojin amma sai muka ga kofar a kulle. Na nuna musu kayan aikina sannan suka barni.

"Bayan shigarmu, mun isa falon Balarabe inda muka samu Wadume da wasu mutane. Na sameshi da ankwa kafa da hannu.

"Bayan na balle ankwar na tafi na barsu."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel