Buhari: Shakka-babu an nada wanda ya dace a kan kujerar NBTE – Inji Obiano

Buhari: Shakka-babu an nada wanda ya dace a kan kujerar NBTE – Inji Obiano

Gwamna Willie Obiano ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan matakin da ya dauka na nada Dr. Nnaemeka Ewelukwa a matsayin shugaban kamfanin NBET.

Willie Obiano ya ce babu wanda shugaban kasar zai nemo wanda ya fi Nnaemeka Ewelukwa dacewa da rike kamfanin NBET mai alhakin saida wutar lantarki a Najeriya.

Gwamnan Anambra ya ce Nnaemeka Ewelukwa kwarare ne wanda ya san aiki da yadda ake gyara. Obiano ya bayyana haka ne a wata wasika da ya aikawa shugaba Muhammadu Buhari.

Kwamishinan harkokin yada labarai na jihar Anambra, C. Don Adinuba, a wani jawabi da ya fitar a makon nan, ya bayyana abin da wasikar da mai gidan na sa ya rubutawa shugaban kasa ta kunsa.

A watan Yuni ne ministan harkar wutar lantarki, Injiniya Saleh Mamman ya bada sanarwar shugaban kasa zai maye gurbin Dr. Marylyn Amobi da Dr. Ewelukwa, wanda dukkaninsu mutanen Anambra ne.

“Ta tabbata cewa shugaban kasa ya duba tasirin NBET a harkar samar da wutar lantarki a Najeriya, don haka ya zabi wanda ya fi kowa dacewa ya canza ragamar harkar wuta.” Inji Obiano.

KU KARANTA: Dalilin fitowa da na yi na godewa Shugaba Buhari - Gwamna Wike

Buhari: Shakka-babu an nada wanda ya dace a kan kujerar NBTE – Inji Obiano
Gwamna Willie Obiano na jam'iyyar APGA
Asali: Depositphotos

“Dr Ewelukwa, ya na rike da mukami a kamfanin NBET na kasa kafin ya samu wannan kujera, kuma ya shafe shekaru goma da su ka wuce ya na kokarin ganin an gyara lantarki a Najeriya.”

Wasikar ta ce: “Sabon shugaban ya yi aiki da kwamitin PTFP wanda Farfesa Bart Nnaji ya jagoranta kafin a nada shi Minista a 2011, inda ya jagoranci sauyin da ba a taba samu ba."

“A matsayinsa na sakataren NBET na farko, ya jagoranci tawagar da ta shiga yarjejeniya da kamfanonin da ke samar da wuta, a dalilin haka ya sa ‘yan kasuwa su ka narka kudinsu.”

“Saboda irin namjin kokarinda masana irinsu Nnaji Dr Ewelukwa su ka yi, gwamnatocin Amurka da Birtaniya su ka taimakawa Najeriya da gudumuwar gyara wuta.” inji Obiano.

Obiano ya bayyana Ewelukwa a matsayin mutum mai saukin kai da bin ka’ida, wanda ya san aiki-tare, sannan kuma mai hangen nesa, da kwarewar aiki a kasashen waje tare da rike mukamai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel