Ba zan fansar da ke da komai a Duniyar nan ba – Ahmed Musa ga Mai dakinsa

Ba zan fansar da ke da komai a Duniyar nan ba – Ahmed Musa ga Mai dakinsa

Kyaftin ɗin ƙungiyar ‘yan wasan ƙwallon ƙafan Najeriya na Super Eagles, Ahmed Musa ya fito gaban Duniya ya na koɗa kyakkyawar mai ɗakinsa da suka ɗauki shekaru uku tare.

Ahmed Musa MON da Miss Juliet Ejue su na bikin shekara uku da aure ne a daidai wannan lokaci. Idan ba ku manta ba, shararrun taurari da manyan ‘yan wasa sun halarci bikin auren na su.

Juliet Ejue ce ta haifawa Ahmed Musa ɗan autansa, kuma bisa dukkan alamu ma’auratan su na zaman lafiya da juna.

Da ya ke magana game da zaman aurensa da Juliet Ejue, fitaccen ɗan kwallon ya ce matarsa ta kawo masa farin ciki a rayuwarsa tun daga ranar da ya fara ɗaga idanuwansa ya gan ta.

Tsohon ɗan wasan na ƙungiyar Leciester City, Ahmed Musa ya ce zai so ya kare rayuwarsa ne da Ejue wanda aka ɗaura masa aure da ita a watan Yulin shekarar 2017

KU KARANTA: Jerin wasu motoci masu numfashi a gidan Ahmed Musa

Ba zan fansar da ke da komai a Duniyar nan ba – Ahmed Musa ga Mai dakinsa
Mai dakin Ahmed Musa, Juliet Ejue. Hoto: Pulse
Asali: Getty Images

‘Dan wasan gaban ya fito shafinsa na Instagram a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, ya na cewa matarsa ce ƙarfinsa, musamman a lokacin da abubuwa ba su tafiya masa daidai.

“Idan na tsaya ina cewa na yi dace da na same ki a rayuwata, ina bata yawu na ne.” inji ɗan wasan ƙungiyar Al Nasr mai shekaru 27.

Ahmed Musa ya kara da cewa matar da ya ke aure a yau, burinsa ce da Ubangiji ya cika masa. Musa ya bayyana cewa zai so ace har abada ya na tare da kyakkyawar uwar yaron na sa.

“Ba zan canza ki da komai a Duniya ba.” inji Ahmed Musa wanda yanzu haka ya ke ƙasar Saudi Arabia kamar yadda shafinsa na Instagram ya bayyana mana.

Daga jiya Laraba zuwa yanzu, fiye da mutane 700 su ka tofa albarkacin bakinsu a kan sakon, bayan mutum kusan 31, 000 da su ka yi sha’awar wannan jawabi a dandalin Instagram.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng