Maganar cewa na sauya-sheka sam ba gaskiya ba ce – Inji Nuhu Ribadu

Maganar cewa na sauya-sheka sam ba gaskiya ba ce – Inji Nuhu Ribadu

- Nuhu Ribadu ya yi magana game da rade-radin cewa ya sake komawa PDP

- Shararren ‘Dan siyasar ya ce har yanzu ya na nan a tafiyar Jam’iyyar APC

- A baya Nuhu Ribadu ya yi ta yawo tsakanin Jam’iyyun ACN, PDP da APC

Ana ta jitar-jitar cewa Nuhu Ribadu ya tsere daga jam’iyyar APC, ya koma goyon bayan gwamnatin jihar Adamawa ta Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP.

Tsohon ‘dan takarar shugaban kasa da kuma gwamna a jihar Adamawa, Nuhu Ribadu ya ce wasu masu neman suna ne su ka saidawa jama’a karyar cewa ya bar jam’iyyar APC.

‘Dan siyasar ya ce daga nan ne wasu su ka fara yawo da wannan jita-jita na cewa ya sauya-sheka.

“Ban taba tunanin masifa za ta sa mutum ya kai ga kitsa irin wannan mummunar furofaganda ba.” Ribadu ya musanya wannnan zargi ne a shafinsa na Twitter a daren Talata.

Ribadu mai shekaru 59, ya tabbatar da cewa shi da jam’iyyar APC mai mulki, mutu ka raba watau takalmin kaza. Ya rubuta: “Babu inda zan je. Ku yi watsi da wannan labari.”

KU KARANTA: APC ba Jam’iyyar siyasa ba ce, taron ganin bayan Jonathan ne - Wike

Maganar cewa na sauya-sheka sam ba gaskiya ba ce – Inji Nuhu Ribadu
Malam Nuhu Ribadu
Asali: Depositphotos

Wata kungiyar siyasa da ke tare da Malam Nuhu Ribadu a jihar Adamawa, ta yi irin wannan martani, ta ce labarin da ake yadawa ba komai ba ne face soki-burutsun banza da wofi.

Mustapha Ribadu wanda shi ne jagoran wannan kungiya ya shaidawa ‘yan jarida a Yola cewa babu gaskiya game da rade-radin da ake yi na cewa mai gidansu ya koma PDP.

“Jagoranmu Mallam Nuhu Ribadu tafiyarsu daya da Buhari. Za mu cigaba da aiki domin nasarar gwamnatin Muhammadu Buhari." Mustapha Ribadu ya ce suna nan kan akidarsu.

Nuhu Ribadu shi ne shugaban EFCC na farko da aka yi a tarihi bayan an kafa hukumar a 2003. A 2011 Ribadu ya yi takara a ACN, a 2014 ya tafi PDP, daga baya ya shiga jam'iyyar APC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel