Idan zan bar mulki ba zan tsaida Magaji ba, shi ke jawo rigima – Inji Nyesom Wike

Idan zan bar mulki ba zan tsaida Magaji ba, shi ke jawo rigima – Inji Nyesom Wike

A ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, gidan jaridar AIT ta yi hira da mai girma gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, inda ya tabo batutuwan da su ka shafi siyasa, gwamnati da ra’ayoyinsa.

Nyesom Wike ya tofa albarkacin bakinsa game da zaben jihar Edo, ya ce: “Ba za a tursasawa jama’a a zaben Edo ba, dole mutane za su fito su zabi wanda su ke so.”

Gwamnan ya ce abokan aikinsa za su dage wajen ganin jam’iyyar PDP ta yi nasara a zaben Jihar Edo. “Duka gwamnonin Kudu maso kudu za su je Edo domin su ba ‘danuwansu gudumuwa.”

Ya ce a zaben 2016, mutanen jihar Edo sun nuna cewa ba su son Fasto Ize-Iyamu, don haka wannan karo PDP ce za ta zama ta karbe mulki a duka jihohin yankin Kudu maso kudu.

Wike ya yi kaca-kaca da jam’iyyar APC mai mulki, ya yi karin haske game da abin da ya jefa jam’iyyar a rikici.

APC ba ta taba zama jam’iyya ba, gungun mutane ne kurum su ka taru domin su tika Goodluck (Jonathan) da kasa.”

“Wannan ya sa jam’iyyar APC ba za ta taba samun hadin-kai ba.”

KU KARANTA: A daina yi wa mutane alfarma wajen neman aiki - Buhari

Idan zan bar mulki ba zan tsaida Magaji ba, shi ke jawo rigima – Inji Nyesom Wike
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
Asali: Twitter

A game da godiyar da aka ji Wike ya na yi wa shugaba Buhari, ya ce wasu kudin ayyuka da gwamnonin jihar su ka yi ne za a maido mata, don haka ya yaba da kokarin gwamnatin tarayya.

Gwamnan ya ce ba a kai ga turo masa wadannan kudi ba, amma an yi masa alkawari, a dalilin haka ya aika budaddiyar wasika ya na yabon gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

"Idan ka yi mana dole mu fada, idan ba ka yi mana ba ma dole mu fada." inji sa.

Wike wanda wa’adinsa zai kare nan da shekaru uku ya ce ba zai tsaida magaji ba. “Idan zan tafi, ba zan fito da ‘dan takara na ba, wannan shi ne abin da ke jawo rikici a jihohi da-dama.”

“Zan bar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, daga wannan lokaci zan rika ganin kai na a matsayin ‘dan kishin kasa ne ba gwamna ba.” Gwamnan ya ce zai cigaba da yi wa mutanesa aiki tukuru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel