Wani kwamishina a jihar Plateau ya kamu da cutar korona

Wani kwamishina a jihar Plateau ya kamu da cutar korona

- Gwamna Simon Lalong ya umurci mambobin majalisar zartarwa ta jihar Plateau da su je su yi gwajin cutar korona bayan wani kwamishina ya kamu da cutar

- Lalong ya kuma bukaci su yi gaggawan killace kansu daga ranar Laraba

- Hakan na zuwa ne bayan kwamishinan kasuwanci da masana’antu, Abe Aku ya kamu da cutar

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya umurci mambobin majalisar zartarwa ta jihar da su je su yi gwajin cutar korona bayan wani kwamishina ya kamu da cutar.

Ya bayyana cewa bayan sun gabatar da kansu domin gwaji su yi gaggawan killace kansu daga ranar Laraba.

Umurnin Lalong na zuwa ne bayan kwamishinan kasuwanci da masana’antu, Abe Aku ya kamu da cutar.

Wani kwamishina a jihar Plateau ya kamu da cutar korona
Wani kwamishina a jihar Plateau ya kamu da cutar korona Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kwamishinan labarai da sadarwa, , Da Manjang, a wani jawabi da ya fitar ya ce: “Bisa ga umurnin gwamnan za a dauki sumfurin kwamishinonin sannan a mika shi ga cibiyar gwajin COVID-19 don gwaji.

“A yayin da ake jiran fitowar sakamakon gwajin ana shawartan jama’a da su guji kai wa mambobin majalisar zartarwar ziyara mara tushe yayinda suke killace kansu.

KU KARANTA KUMA: Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa

"Bayan dakile yiwuwar yaduwar cutar da hakan zai yi, zai kuma yi nuni ga koyarwar shugabanci nagari.”

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an tabbatar da cewar Gwamna Lalong da iyalansa basa dauke da cutar bayan gwajin da aka yi masu.

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin yaki da cutar korona na fadar shugaban kasa, Boss Mustapha a ranar Alhamis ya ce za a sake kulle Najeriya da yana da karfin ikon aikata hakan.

Mustapha ya ce duk da ba za a so komawa kullen ba, shine abinda yafi cancanta idan aka duba halayyar wasu 'yan Najeriya.

Kwamitin yaki da cutar na ci gaba da jajanta yadda 'yan Najeriya ke watsi da dokokinsu na dakike yaduwar cutar.

A yayin jawabi a taron su, SGF ya jajanta yadda wasu jama'a ke kai wa cutar korona runguma kamar a wasan kwaikwayo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel