Orji Kalu ya gabatar da kudirin gyara dokar ACJ-2015 a gaban Majalisar dattawa

Orji Kalu ya gabatar da kudirin gyara dokar ACJ-2015 a gaban Majalisar dattawa

A ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2020, majalisar dattawan Najeriya ta karbi kudirin da ke neman yi wa dokar masu laifi watau ACJ ta shekarar 2015 kwaskwarima.

Jaridar Daily Trust ta ce a yau ne aka fara sauraron wannan kudiri a zauren majalisar tarayyar.

Wanda ya gabatar da kudirin shi ne Sanatan jam’iyyaar APC mai wakiltar yankin Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu.

A Disamban 2019 kotu ta samu Orji Uzor Kalu da laifin satar kudi daga baitul-mali a lokacin da ya ke gwamnan jihar Abia. Wannan ya sa aka rufe Sanatan a gidan yarin da ke garin Kuje.

Daga baya kotun koli ta soke shari’ar da aka yi wa tsohon gwamnan da sunan cewa bai kamata Alkalin ya zauna a kotun ba. A dalilin haka aka wargaza hukuncin daurin shekaru 12 da aka yanke masa.

Fitowar Sanata Orji Uzor Kalu ke da wuya daga kurkuku, ya fara kokarin kawo yadda za a gyara sha’anin gidajen yari a Najeriya bayan ya gane ma kansa yadda abubuwa su ke a kasar.

KU KARANTA: A dakatar da shirin daukar Matasa 774, 000 aiki - Majalisa

Orji Kalu ya gabatar da kudirin gyara dokar ACJ-2015 a gaban Majalisar dattawa
Sanata Orji Uzor Kalu
Asali: Twitter

Kalu ya ce zamansa a gidan kaso ya nuna masa irin rashin adalcin da mutane su ke fuskanata wajen shari’a, ya sha alwashin tsayawa tsayin daka wajen ganin ya kare wadanda su ke neman gaskiya a kotu.

Babban Sanatan na APC ya ke cewa: “Adalci ga mutum guda ko tsirarun mutane ba zai isa a kasar nan ba.”

“Tsarin da za ace fiye da 70% na mutanen da ke cikin gidajen kurkuku, su na jiran a yanke masu hukunci ne ba zai cigaba ba.” Inji ‘dan majalisar tarayyan.

“Halin da mu ka samu kanmu idan wadanda ba su aikata laifi ba su ke amsa zargin kisan kai ba zai cigaba ba, wannan ba ya nuna darajar kasarmu.”

Sanata Kalu ya ce: “Dole ayi wa kowa adalci. Wannan shi ne shirin da na dauka ga ‘yan Najeriya.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng