Rashin tsaro: Buratai ya bude babban sansanin sojoji na musamman a Katsina

Rashin tsaro: Buratai ya bude babban sansanin sojoji na musamman a Katsina

Shugaban rundunar sojojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, ya bude babban sansanin sojoji na musamman a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

Samar da sansanin na daga cikin bikin zagayowar ranar dakarun sojin sama na 2020, wanda ake yi a jihar Katsina don yakar 'yan bindiga da dukkan matsalolin tsaro da ya addabi yankin arewa maso yamma.

Buratai yace: "Za a kaddamar da manyan ayyukan a yankunan kasar nan shida. Ana yin haka ne don inganta dangantakar da ke tsakanin farar hula da soji.

"Dakarun za su raba kayan tallafi ga mabukata a fadin jihohi 36 na kasar harda babban birnin tarayyar kasar."

Rashin tsaro: Buratai ya bude babban sansanin sojoji na musamman a Katsina
Rashin tsaro: Buratai ya bude babban sansanin sojoji na musamman a Katsina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Buratai ya kara da cewa za a kaddamar da sabon atisaye mai suna SAHEL SANITY wanda amfaninsa shine yakar ayyukan 'yan bindiga da dukkan masu laifi a fadin arewa maso yamma.

Ya ce a bikin wannan shekarar, ba za a yi da tsofaffin soji ba saboda gudun barkewar annobar. Ya ce za a fitar da lokacin da ya dace don bikin jinjina musu bayan annobar.

Ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa dakarun basu amsa kiran gaggawa idan aka yi musu a yankunan da babu zaman lafiya, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Ya yi jan kunne a kan siyasantar da tsaron Najeriya baki daya.

Yankin arewa maso yamma na kasar nan, musamman jihar Katsina na fuskantar babban matsala na tsaro.

KU KARANTA KUMA: Kudin wuta: Shugabannin majalisa sun hadu da Buhari don saukakawa talakawa

A ranar Litinin, Gwamna Aminu Bello Masari ya sanar da Buratai cewa mazauna jihar musamman na kusa da daji suna cikin tsoro da rashin tabbas.

Dajin rugu da ya ratsa ta kananan hukumomi takwas da suka hada da Jibia, Safana, Danmusa, Hatsari, Dandume, Sabuwa, Kankara da Faskari ya zama maboyar 'yan bindigar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ya bai wa rundunar soji umarnin gamawa da 'yan bindiga da ke kashe 'yan jihar.

Ya kara da cewa kada a bar dan bindiga ko daya da rai.

Masari ya yi wannan kiran ne yayin da ya kai ziyara ga 'yan gudun hijira a kananan hukumomin Faskari, Kadisau da Dandume na jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel