Zulum ya sanar da lokacin jana'izar tsohon shugaban ma'aikata Dakta Babagana
Allah ya yi wa tsohon shugaban ma'aikatan jihar Borno, Dakta Babagana Wakil, rasuwa a yau, Laraba, 1 ga watan Yuli, kamar yadda sanarwa daga gwamnatin jihar Borno ta bayyana.
A cikin wani jawabi mai dauke da sa hannun Isa Gusau, ma'aikacin sashen watsa labarai a gidan gwamnatin Borno, gwamnan jihar, Farfesa Babagana Umar Zulum, ya sanar da cewa za a yi jana'izar marigayin da yamma.
Da ya ke kara yada labarin mutuwar Dakta Wakil a shafinsa na Tuwita, Farfesa Zulum ya ce za a yi jana'izarsa a gidansu na gado da ke unguwar Shehuri ta arewa a birnin Maiduguri.

Asali: Facebook
Gwamna Zulum ya yi addu'ar Allah ya ji kansa, ya yafe kura-kuransa, ya bawa iyali da danginsa hakurin jure rashinsa.
Sai dai, sanarwar ba ta yi karin bayani dangane da sababin mutuwar Dakta Wakil ba.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng