Rikicin APC: Jam'iyya ta fara sasancin 'ya'yanta da ke fadin kasar

Rikicin APC: Jam'iyya ta fara sasancin 'ya'yanta da ke fadin kasar

- Jam'iyyar APC ta bayyana shirinta na dawo da zaman lafiya a jam'iyyar mai mulki tun kafin zuwan zabe na gaba

- Jam'iyyar ta kafa kwamitin mai dauke da mambobi don sasanci da za a yi a babban ofishin jam'iyyar na kasa da ke Abuja

- Kwamitin ya rungumi tsari shida don aiki da su a taron rantsarwar da aka yi

Jam'iyyar APC ta tsara yadda za ta dawo da zaman lafiya a tsakanin 'ya'yanta don samun damar lashe zabukan jihohin Edo da Ondo da ke karatowa.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ce jam'iyyar za ta hanzarta sasanta 'ya'yanta a duk fadin kasar nan don dawo da zaman lafiya tare da lumana, jaridar The Nation ta ruwaito.

Rikicin APC: Jam'iyya ta fara sasancin 'ya'yanta da ke fadin kasar
Rikicin APC: Jam'iyya ta fara sasancin 'ya'yanta da ke fadin kasar Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

A ranar Litinin, 29 ga watan Yuni, jam'iyyar ta kafa kwamitin sasanci a babban ofishin jam'iyyar da ke Abuja.

Ta fidda tsari shida wanda za ta yi amfani da su wurin gyara zaman jam'iyyar a taron rantsarwar da aka yi wa 'yan kwamitin rikon kwaryar.

KU KARANTA KUMA: Yadda zan tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci - Buhari

Jam'iyyar ta amince da kafa kwamitin kamfen da zaben gwamnan jihar Edo tare da sasanci.

Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya yi kira ga 'yan jam'iyyar da su bai wa mambobin kwamitin hadin kai don ganin daidaituwar jam'iyyar kafin zaben 2023.

A wani labari na daban, mun ji cewa jam’iyyar PDP ta shawarci mataimakin gwamnan jihar Ondo, Agboola Ajayi da ya yi murabus tunda ya bar jam’iyyar APC da aka zabesa a karkashinta.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na yankin kudu maso yamma, Ayo Fadaka, ya bayyana hakan yayin zantawa a Sunrise Daily na gidan talabijin din Channels.

Kakakin jam’iyyar PDP ya kara da cewa, ya rage ga gwamnan da kuma jam’iyyar APC Ko za su ci gaba da zama da Ajayi a matsayin mataimakin gwamnan duk kuwa da sauya shekar da yayi.

Ya ce, kamata yayi Ajiyi ya yi abinda ya dace ta hanyar yin murabus hankali kwance tunda ba zai iya tafiya daya da gwamnan ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel